Babu Wasa: Sabon Shugaban 'Yan Sanda Ya Sanar da 'Yan Najeriya Shirinsa bayan Fara Aiki

Babu Wasa: Sabon Shugaban 'Yan Sanda Ya Sanar da 'Yan Najeriya Shirinsa bayan Fara Aiki

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta samu sabon shugaban da zai jagorance ta bayan murabus din Kayode Egbetokun
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Olatunji Disu a matsayin sabon mukaddashin shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya
  • Olatunji Disu ya bayyana cewa bai yi tsammanin samun wannan mukami mai girma daga wajen Shugaba Bola Tinubu ba

​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mukaddashin shugaban ’yan sandan Najeriya (IGP), Olatunji Disu, ya yi magana bayan ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Olatunji Disu ya bayyana cewa zamanin yin ba dai-dai da kuma rashin bin doka a rundunar ’yan sandan Najeriya ya zo karshe.

Sabon mukaddashin IGP ya yi rantsuwar kama aiki
Sabon mukaddashin shugaban 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Sufeta Janar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan rantsar da shi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, a ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya tura jakadu lungu da sako, za su isar da sako ga 'yan Najeriya

Olatunji Disu wanda saura masa 'yan kwanaki ya yi ritaya daga aiki ya yi mamakin nadinsa bayan magabacinsu ya gabatar da takardar murabus.

Mukaddashin IGP din ya bayyana cewa naɗin ya zo ne a daidai lokacin da ba ya tsammaninsa.

Ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda shugaban kasar yake magana kan ayyukan da ya yi da nasarorin da ya samu a wurare da dama.

"Yadda yake ambatar ayyuka na da dama, yana ambatar wuraren da na yi aiki, da kuma nasarorin da na samu a matsayina na ɗan sanda, ya taɓa zuciyata sosai, har kusa na yi kuka."

- Olatunji Disu

Me shugaban 'yan sanda ya ce kan Tinubu?

A cewarsa, wannan ya nuna cewa shugaban kasar ya ɗauki lokaci yana sa ido kan jami’an da ke aiki a ko ina a faɗin kasar, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

“Wannan ya nuna cewa shugaban kasar ya ba ni ƙalubalen na je na yi abin da aka san ni da shi, kuma na tabbatar na samar da zaman lafiya da kuma karrama ƙasar nan.”

Kara karanta wannan

Kurunkus: Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban Rundunar 'Yan Sandan Najeriya

- Olatunji Disu

Olatunji Disu ya kama aiki a matsayin mukaddashin IGP
Olatunji Disu tare da tsohon IGP, Kayode Egbetokun wajen karbar ragamar aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Sakon sabon IG ga jami'an 'yan sanda

Game da saƙon da zai isar ga jami’ai da dakarun rundunar yayin da ya fara aiki, sai sabon mukaddashin IGP din ya ce:

“Zan sanar da su cewa zamanin nuna isa da rashin bin doka ya kare. Zan tabbatar na horar da su tare da karfafa gwiwarsu wajen ganin sun kiyaye hakkokin ɗan adam."
“Zan tabbatar sun sani cewa zan bi tsarin rashin amincewa da kowane irin cin hanci da rashawa. Kuma mafi mahimmanci, zan koya musu cewa ba za mu taɓa yin nasara ba idan babu haɗin kan al’umma.”

- Olatunji Disu

Dalilin murabus din shugaban 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan dalilin murabus din shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun.

Kayode Egbetokun ya ajiye aikinsa ne a ranar Talata 24 ga watan Fabrairun shekarar 2026 bayan ya yi wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Bayo Onanuga wanda ke ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai ya ce dalilan yin murabus din Egbetokun ya shafi iyalinsa ne da ke buƙatar cikakkiyar kulawarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng