Akwai Kura: Ministan Tinubu Na cikin Matsala, Kotu Amince a Yi Bincike Kansa

Akwai Kura: Ministan Tinubu Na cikin Matsala, Kotu Amince a Yi Bincike Kansa

  • Wani dan gwagwarmaya ya garzaya babbar kotun tarayya da bukatunsa kan Ministan harkokin ciin gida, Olubunmi Tunji-Ojo
  • 'Dan gwagwarmayar na neman kotu ta amince a binciki takardun shaidar karatu na Ministan wanda a baya ya taba zama 'dan majalisar wakilai
  • Kotun ta amince da bukatar 'dan gwagwarmayar, yayin da wata kotun ta daban ta ki amincewa da wata bukata da ya nema

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babban kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar da aka shigar a gabanta kan Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Babbar kotun ta amince da neman izinin bincikar takardun shaidar karatu na Olubunmi Tunji-Ojo.

Kotu ta amince a binciki takardin Olubunmi Tunji-Ojo
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo Hoto: Hon Olubunmi Tunji-Ojo
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce alkalin kotun, mai shari'a Binta Nyako, ta amince da bukatar a ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairun 2026. kotun, mai shari'a Binta Nyako, ta amince da bukatar a ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Samha Inuwa: Kotu ta yanke wa fitacciyar jarumar Kannywood hukuncin ɗaurin wata 6

An amince a binciki Ministan Tinubu

Binta Nyako ta amince ne da buƙatar wadda wani mai fafutuka, Emorioloye Owolemi, ya shigar, inda yake neman a bincika sahihancin takardar shaidar kammala sakandare (WAEC) da ministan ya samu.

A cikin buƙatar da lauyansa, Philemon Yakubu (SAN) ya gabatar, Owolemi ya nemi izinin ne ta hanyar wani ƙuduri da aka shigar bisa ga tsarin dokokin babban kotun tarayya na 2019, da kuma sassan 1, 20, da 21 na dokar ’yancin samun bayanai na 2011.

Kotu ta ki yarda da wata bukatar lauya

Sai dai kuma, wata kotun tarayyar daban ƙarƙashin mai shari'a Joyce Abdulmalik, ta ki amincewa da wata buƙatar ta biyu da ke neman bincikar halaccin takardar kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC) ta ministan, jaridar The ta kawo labarin.

Game da buƙatar binciken NYSC ɗin da aka yi watsi da ita, Owolemi ya nemi umarnin kotu ne domin tilasta wa hukumar NYSC ta ba shi bayanan da ya nema a cikin wasiƙarsa ta ranar 17 ga Nuwamba, 2025, game da takardar kammala NYSC ta Ministan da ke hannun hukumar.

Kara karanta wannan

Atiku ya samu abokin takara don fafatawa a zaben 2027? An ji yadda lamarin yake

Me aka bukata kan Olubunmi Tunji-Ojo?

Daga cikin abubuwan da mai ƙarar ya nema, har da tilasta wa NYSC ta bayar da bayanan tantancewa na kowane wata, inda Ministan ya yi hidima kafin zargin guduwa ba tare da izini ba.

Ya bukaci a ba shi bayanan asusun banki, bayanan kuɗi na rajistar NYSC ta shekarar 2006, da dukkan bayanan biyan alawus na kowane wata, gami da kwanakin biya, adadin kuɗi, da asusun da aka tura wa kuɗaɗen.

Kotu ta ki amincewa da bukatar da aka shigar kan Tunji Ojo
Olubunmi Tunji-Ojo, Ministan harkokin cikin gida a Najeriya Hoto: Hon Olubunmi Tunji-Ojo
Source: Facebook

Sauran bayanan sun haɗa da takardun NYSC na hukuma da ke bayyana kwanan wata, yanayi, da matsayin zargin guduwar Ministan daga aiki, da dukkan wasiƙun cikin gida, tambayoyi, rahotan hukunci ko wasiƙun da aka yi a kan hakan, sannan da takardun rajista, tura aiki, da na hidimar shekarar 2006.

A halin yanzu, mai shari,'a Binta Nyako ta sanya ranar 14 ga Maris domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Kungiya ta bukaci Tinubu ya kori Tunji-Ojo

A wani labarin kuma, kun ji cewa an bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kori Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: NNPP ta yi martani mai zafi da Amurka ta kawo batun kakaba wa jagoranta takunkumi

Kungiyar ta yi zargin cewa takardar shaidar kammala NYSC da Ministan ya gabatar na dauki da kura-kurai kuma ta bogi ce.

Sun kuma bayyana cewa ci gaba da barin Olubunmi Tunji-Ojo a mukaminsa na Ministan harkokin cikin gida babban nakasu ga kasa ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng