Sanatan da Ya Rasa Dan'uwansa a hannun 'Yan Bindiga, Ya Gano Hanyar Magance Rashin Tsaro

Sanatan da Ya Rasa Dan'uwansa a hannun 'Yan Bindiga, Ya Gano Hanyar Magance Rashin Tsaro

  • Sanata Garba Maidoki wanda ke wakiltar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, ya koka kan matsalar rashin tsaro
  • Garba Maidoki ya bayyana cewa samar da tsaro ga al'umma ya fi muhimmanci fiye da samar da ababen more rayuwa idan har babu kwanciyar hankali
  • Sanatan ya bayyana cewa sojojin da ake da su a kasar nan, sun yi kadan wajen yakin da ake yi da ayyukan 'yan bindiga

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Garba Maidoki, Sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, Garba Maidoki, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.

Sanata Garba Maidoki ya yi kira da a kara yawan sojoji da kuma kuɗaɗen da ake bai wa rundunar sojojin Najeriya, domin su samu damar magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Katsina ya girgiza majalisa, ta mika bukata wajen Tinubu

Sanata Garba Maidoki ya koka kan rashin tsaro
Sanata Garba Maidoki a zauren majalisar dattawa Hoto: Senator Garba Maidoki
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce Garba Maidoki ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026 yayin zaman majalisar dattawa.

Me Maidoki ya ce kan rashin tsaro?

Sanatan ya ce ya kamata tsaro ya fi samun muhimmanci fiye da ababen more rayuwa, musamman idan ana tilasta wa al’umma barin gidajensu saboda rashin tsaro.

"A baya mun amince cewa a ƙara kuɗin da ake bai wa sojoji. Wannan lokaci ne na kasafin kuɗi. Na faɗa cewa idan ka gina mani makaranta yau, amma na gudu daga wannan makaranta, babu amfaninta a gare ni."
"Idan ka gina mani hanya, amma na gudu daga wannan yankin, hanyar ba ta da amfani a gare ni. Abin da nake so shi ne a tabbatar da tsaro. Ina so a tsare ni, a tsare mutanena.”

- Sanata Garba Maidoki

Sanata Maidoki ya yaba wa sojoji

Ya yaba wa rundunar sojojin Najeriya bisa ƙoƙarin da suke yi, amma ya jaddada cewa sun yi ƙaranci sosai wajen yawan ma’aikata.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun fara aiki a kan sabon kudirin da zai kara wa gwamnatin tarayya kudi

Sanata Garba Maidoki ya kuma bayyana cewa kwanan nan ya rasa ɗan uwansa sakamakon matsalar tsaro.

“Sojoji suna ƙoƙari matuƙa, amma ba su da isassun ma’aikata. Kwana uku da suka wuce, na rasa ɗan uwana wanda jami’in soja ne a wannan yaƙin da ake da ’yan bindiga; ya rasu yana yaƙi da ’yan bindiga. Kuma ina alfahari da shi.”

- Sanata Garba Maidoki

Sanata ya ce akwai karancin sojoji

Sanatan na Kebbi ya ce adadin sojojin Najeriya a halin yanzu ya yi kadan domin tinkarar matsalar ’yan bindiga a faɗin ƙasar.

“Idan ba mu ƙara yawan sojojin da za su kula da tsaron ƙasar nan ba, sojoji kusan 230,000 da muke da su a 2025 ba za su iya magance wannan matsalar ’yan bindiga ba."

- Sanata Garba Maidoki

Sanata Garba Maidoki ya kuma nuna damuwa kan tsawon lokacin da ake ci gaba da yaƙi da ’yan bindiga.

“Ba zai yiwu mu riƙa yaƙi da ’yan bindiga na tsawon shekara 20 ba. Har yaushe muke so mu ci gaba da tafiya da wannan matsala?”

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi abin zai ba Tinubu damar cin zabe cikin sauki a 2027

- Sanata Garba Maidoki

Garba Maidoki ya ce akwai karancin sojoji a Najeriya
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki Hoto: Senator Garba Maidoki
Source: Facebook

Wace shawara 'dan majalisa ya ba da?

A karshe, Maidoki ya bukaci majalisar dattawa da ta ba da fifiko ga kuɗaɗen sojoji a kasafin kuɗin da ke tafe.

"Mu sanya isassun kudade, kasafin kuɗi na zuwa gabanmu, mu sanya kuɗi sosai domin rundunar sojoji."

- Sanata Garba Maidoki

'Yan bindiga sun kai hari a Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wasu kauyuka na jihar Kwara.

Maharan sun farmaki garuruwan Woro da Nuku inda suka kashe aƙalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.

Baya ga kisan kai, maharan sun kona gidaje da dama, lamarin da ya sa mutane da yawa rasa matsugunansu a kauyukan na karamar hukumar Kaiama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng