Zargin Lalata da Matar Aure: Magidanci Ya Sassara Wani Mutum da Adda har Lahira
- Rundunar yan sandan Jihar Yobe ta kama Alhaji Hassan Umaru mai shekaru 50 bisa zargin sassara wani mutumi da adda har ya mutu
- Lamarin ya afku ne a dandalin kasuwar kauyen Bundila, inda Alhaji Hassan ya kashe Sukari Abdul saboda zargin yana neman matarsa
- Kwamishinan yan sanda ya gargadi mazauna jihar da su guji daukar doka a hannunsu su yayin da ake shirin gurfanar da Hassan gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da kama wani mutum mai shekaru 50, Alhaji Hassan Umaru, bisa zargin kashe Sukari Abdul.
Hassan Umaru ya sanya adda, ya sassari Sukari Abdul mai shekaru 45 da suka fito daga kauye daya saboda zargin yana lalata da matarsa.

Source: Original
Kakakin rundunar 'yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a ranar 1 ga watan Fabrairu, 2026, a kauyen Bundila, in ji rahoton Punch.
Abin da ya jawo kisan kai a Yobe
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya barke ne da misalin karfe 12:30 na rana a dandalin kasuwar garin dake karamar hukumar Gulani.
Zargin cin amanar aure ne ya janyo cacar baki wadda daga baya ta rikide zuwa kazamin fada tsakanin mutanen biyu a bainar jama'a.
A lokacin da suka yi taho-mu-gama, magidancin ya yi amfani da adda inda ya sassara wanda yake zargin a gaban jama'a.
An garzaya da Sukari Abdul zuwa cibiyar lafiya ta matakin farko dake Bularaba domin ceto rayuwarsa bayan samun raunukan. Sai dai likita ya tabbatar da cewa ya mutu jim kadan bayan isarsa asibitin.
Matakin da 'yan sanda suka dauka
SP Abdulkarim ya tabbatar da cewa jami'an tsaro sun yi nasarar cafke Alhaji Hassan Umaru tare da kwato addar da ya yi kisan da ita.
An mayar da maganar zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jiha (SCID) domin gudanar da bincike mai zurfi kan wannan danyen aiki.
Kwamishinan 'Yan sandan jihar, Emmanuel Ado, ya nuna bacin ransa tare da yin gargadi mai tsanani ga mazauna jihar baki daya.
Ya ce:
"Kwamishinan na jan kunnen jama'a da kada su rika daukar doka a hannunsu, musamman wajen magance matsalolin aure ko na zaman takewa."

Source: Twitter
Daga zargi sai kisan kai
Ya kuma bukaci mutane da su rika kai korafe-korafensu ga hukumomin da suka dace maimakon amfani da karfi ko makami, in ji rahoton The Eagle Nigeria.
Wannan lamari ya tayar da hankalin mazauna kauyen na Bundila, inda mutane ke jimamin yadda zargin ya kai ga jawo asarar rai.
A halin yanzu, wanda ake zargin ya aikata kisan yana hannun 'yan sanda inda ake jiran kammala bincike kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.
Ango ya cakawa amarya wuka har lahira
A wani labari, mun ruwaito cewa, wani matashi dan shekara 25, Sufiyanu Aliyu ya halaka matarsa da wuka yayin da sabani ya shiga tsakaninsu a jihar Sakkwato.
Rundunar yan sanda ta kama wanda ake zargin tare da wukan da aka aikata laifin domin gudanar da bincike da gurfanar da shi a kotu.
Kwamishinan yan sanda na reshen jihar Sakkwato, CP Ahmed Musa ya tabbatar wa jama'a cewa za a yi wa marigayiyar adalci yayin da ake ci gaba da bincike.
Asali: Legit.ng

