A Karshe, An Ji Abin da Ya Taimaka Aka Gano Shirin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

A Karshe, An Ji Abin da Ya Taimaka Aka Gano Shirin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

  • Janar Christopher Musa ya yi bayanin yadda jami'an tsaro suka hada kai, har suka gano shirin da aka yi na kifar da gwamnatin Bola Tinubu
  • Ministan tsaron ya musanta cewa an shirya kifar da Tinubu ne saboda halin da kasa ke ciki, ya ce tun kafin ya hau mulki aka fara kitsa makarkashiya
  • A watan Oktoba, 2025 ne aka fara jin kishin-kishin din juyin mulki amma rundunar sojojin Najeriya ta musanta lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda asirin wadanda suka fara kitsa juyin mulki ya tonu tun kafin su aiwatar da shirinsu a aikace.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa an gano shirin hambarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ta hanyar hadin gwiwar sa ido tsakanin hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda aka tsara harbe ministan tsaro, Janar Christopher Musa

Janar Musa.
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Hoto: @storiman
Source: Twitter

Yadda aka dakile shirin juyin mulki

A rahoton The Nation, Janar C.G Musa ya ce wannan hadin gwiwa ne ya bai wa Rundunar Sojin Najeriya damar dakile yunkurin juyin mulki da aka shirya.

A cewarsa, wani Kanal da ya ji haushin faduwa jarabawar karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar, shi ne ya kaddamar da shirin juyin mulkin tare da jawo wasu mutane ciki.

Jita-jitar yunkurin juyin mulki ta fara yaduwa ne a watan Oktoban bara, amma a wancan lokaci Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta musanta batun, tana cewa babu wani abu makamancin haka.

Sai dai a watan da ya gabata, DHQ ta tabbatar da cewa lallai an yi yunkurin juyin mulki, inda bincike ya gano jami’an sojoji 16 da ake zargin suna da hannu a ciki, wadanda yanzu za a gurfanar da su gaban kotun soja.

Abin da ya sa sojoji suka boye lamarin

Ministan tsaro ya bayyana cewa ba a gaggauta tabbatar da yunkurin juyin mulkin ba tun farko domin bai wa hukumomi damar gudanar da cikakken bincike, gano wadanda ke da hannu a ciki, tare da kauce wa kama wadanda ba su da laifi.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Ministan tsaro ya faɗi hukuncin da ke jiran sojojin, ya yi albishir ga iyalansu

A cewarsa, ya fi dacewa a dakata har sai an fahimci yadda aka tsara shirin da kuma wadanda suka dauki nauyinsa kafin a fito fili a tabbatar da batun.

Ya bayyana masu shirin juyin mulkin a matsayin “mutane marasa muhimmanci”, yana mai cewa sun raina karfin dimokuradiyyar Najeriya da hadin kan sojoji.

Matakin da aka dauka tun farko

Musa ya kara da cewa hukumomin tsaro sun rika sa ido a kansu a hankali domin tattara kwararan hujjoji kafin daga bisa aka rusa shirin juyin mulkin nasu gaba daya.

Binciken ya nuna cewa an fara tsara yunkurin juyin mulkin tun kafin zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2023.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jagorantar wani zama a fadarsa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Janar Musa ya karyata ikirarin cewa an shirya yi wa Tinubu juyin mulki ne saboda halin kuncin da jama'a ke ciki a mulkinsa, yana mai cewa:

“An kulla wannan makarkashiya ne tun kafin shugaban kasa ya hau mulki, bayan an tabbatar da ya lashe zabe.”

Ya ce shirin na iya jawo zubar da jini mai yawa, amma an samu nasarar tarwatsa shi tun da wuri kafin aiwatarwa.

Juyin mulki: Yadda aka tsara harbe Janar Musa

Kara karanta wannan

Abin da aka tanadar wa iyalan sojojin da suka yi yunkurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki

A wani labarin, kun ji cewa Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa yana cikin mutanen da masu yunkurin juyin mulki suka sanya a jerin waɗanda za a harbe.

Janar Musa ya ce masu shirin juyin mulkin sun yi niyyar cafke shi, kuma idan ya ƙi amincewa da hakan, za a harbe shi har lahira.

Ya ce yin tunanin cewa za a iya aiwatar da juyin mulki a Najeriya a wannan lokaci kuskure ne babba, yana mai cewa masu wannan tunanin suna bukatar su sake nazari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262