Cikakken Bayani: Dalilin da Ya Sa Za a Gudanar da Azumin Ramadan sau 2 a 2030

Cikakken Bayani: Dalilin da Ya Sa Za a Gudanar da Azumin Ramadan sau 2 a 2030

  • Masana sun yi hasashen cewa za a azumci Ramadan sau biyu a shekarar 2030 saboda bambancin da ke tsakanin kalandar Hijira da ta Miladiyya
  • Ramadan wata ne na tara a kalandar Musulunci, kuma ranakun watan kan canza kowace shekara saboda kalandar na bin zagayowar wata
  • Musulmai suna yin azumi na kwanaki 29 ko 30 a cikin watan Ramadan, inda suke kame baki daga fitowar alfijir, su sha ruwa bayan faduwar rana
  • Musulman da Allah ya yi tsawon rayuwarsu suka kai 2030, za su yi azumi sau biyu a shekarar, abin da ke faruwa duk bayan shekaru 30 kadai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ramadan wata ne na tara a kalandar Musulunci. Duk shekara, ranakun Ramadan kan canza saboda an gina kalandar Musulunci bisa zagayowar wata.

Watan Ramadan yana daukar kwanaki 29 ko 30, inda Musulmai ke yin azumi daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana kowace rana.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jefa kasar Nijar wahalar fetur har ta nemi agajin Najeriya

Rahoto yayi bayanin yadda za a azumci Ramadan sau biyu a shekarar 2030
Rahoto yayi bayanin yadda za a azumci Ramadan sau biyu a shekarar 2030. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ana sa ran yin azumi 2 a shekarar 2030

A daren 27 ga Ramadan, Musulmai na gudanar da ibada ta musamman domin neman dacewa da Lailatul Qadr, wanda ya zama dare mai dumbin daraja, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kammala azumin Ramadan, ana gudanar da bikin karamar Sallah (Eid al-Fitr), wanda ke nuna karewar azumi, inda Musulmi ke gudanar da bukukuwan murnar Sallah.

Masana ilimin taurari da malaman addini sun yi hasashen cewa za a yi Ramadan sau biyu a shekarar 2030, watau nan da shekara biyar.

Abin da zai jawo yin azumi 30 a 2030

Hakan ya faru ne saboda bambancin da ke tsakanin kalandar Hijira da ta Miladiyya, wacce ake lissafinta bisa zagayowar rana.

Wannan bambanci yana sa Ramadan ya fado sau biyu a cikin shekarar Miladiyya duk bayan kimanin shekaru 30, in ji wani masanin taurari a wani bidiyo da ya fitar.

Kara karanta wannan

Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu

Rahoton ICIR ya nuna cewa, karon karshe da hakan ya faru shi ne a shekarar 1997, kafin hakan a shekarar 1965, sannan kuma zai sake faruwa a shekarar 2063.

A shekarar Hijira ta 1451 AH, ana hasashen watan Ramadan zai fara a ranar 5 ga Janairu, 2030, sannan a shekarar 1452 AH zai fara a ranar 26 ga Disamba, 2030.

Watan miladiyya da za a yi karamar Sallah a 2030

Wannan yana nufin cewa a shekarar 2030, Musulmai za su yi azumi na kusan kwanaki 36 gaba ɗaya: watan Ramadan na kwanaki 30 a shekarar 1451 AH da kuma kusan kwanaki 6 na shekarar 1452 AH.

Ana sa ran gudanar da bikin karamar Sallah zai kasance a watan Fabrairu, 2030, kamar yadda rahoton kalandar ya nuna.

Kamar yadda aka saba, za a tabbatar da ranakun Ramadan da Eid ne bayan ganin jinjirin wata, wanda hukumomin addini a kasashe daban-daban ke tantancewa.

Kara karanta wannan

Albashi N500,000: 'Yan kasar Sin suka shigo Najeriya, sun kafa kamfanin sarrafa lithium a Nasarawa

Mutanen da azumi ya fadi a kan su

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sheikh Aminu Daurawa ya lissafa wasu jerin wasu mutane 12 da shari’a ta daukewa nauyin azumi saboda wasu dalilai.

Daga cikin wadannan mutane da suka hada da mata masu jinin al'ada, matafiya, marasa lafiya; akwai wadanda za su rama azumi, akwai wadanda su yi ciyarwa kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Tags: