Mun shiga yanayi mai muni, Najeriya zata iya tarwatsewa kafin 2030, Sanata

Mun shiga yanayi mai muni, Najeriya zata iya tarwatsewa kafin 2030, Sanata

  • Sanata mai wakiltar jihar Benuwai ta arewa, Gabriel Suswam, yace Najeriya ta faɗa cikin wani yanayi mafi muni
  • Sanatan, wanda tsohon gwamnan jihar Benuwai ne, yace a kullum Najeriya ƙara tsunduma take cikin matsala kala daban-daban
  • Yace matukar shugabanni ba su ɗauki matakin da ya dace ba, to akwai tantamar Najeriya zata cigaba da zama ƙasa ɗaya nan da shekara 10

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Gabriel Suswam, yace Najeriya ba zata cigaba da zama ƙasa ɗaya ba nan da shekara 10 matukar shugabanni basu tashi tsaye ba wajen ceto ƙasar daga halin da ta shiga.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da wani littafi a Abuja, ranar Asabar, Suswam ya bayyana cewa Najeriya na ƙara tsunduma ne saboda haka akwai bukatar a samu canji, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ai ba a yin dole a siyasa – Tsohon Gwamnan Arewa ya yi wa Gwamnonin Kudu raddi

Gabriel Suswam
Mun shiga yanayi mai muni, Najeriya zata iya tarwatsewa kafin 2030, Sanata Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

A rahoton This Day, Suswam, wanda sanata ne mai wakiltar arewa maso gabashin jihar Benuwai, yace akwai jan aiki a gaban shugabannin siyasa.

Yace akwai bukatar shugabannin siyasa su jawo matasa a jiki kuma su sanya su a cikin jagorancinsu.

Yaushe Najeriya zata fita daga wannan yanayin?

"Lokaci na tafiya, rayuwa na ƙara kunci ga yan Najeriya, kuma babu tabbacin yaushe yan Najeriya zasu fita daga wannan ƙalubalen. Babu tabbacin Najeriya zata cigaba da zama ƙasa ɗaya nan da shekara 10 matukar ba'a yi abinda ya dace ba."
"Matsalolin tsaro sun yi yawa, ga matsalar tattalin arziki, a halin yanzun Najeriya ta faɗa cikin yanayi mafi muni kuma bamu san ranar fita ba."
"Mun tsinci kan mu a wani yanayi da muke bukatar canji daga inda muke a yau. Kowa yasan cewa komai ya yi karanci, kasafin kudin Najeriya tun 2015 zuwa yau baya isa."

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Ina mafita?

Sanata Suswam ya ƙara da cewa abinda ya kamata shugabanni su yi yanzun shine koyar da matasan yanzun harkokin yau da kullum.

A cewarsa horad da matasa akan harkokin siyasa da sauransu zai taimaka matuƙa wajen dawo da ƙasar nan kan turabr da ya dace.

"Idan bamu kula da matasan mu yadda ya dace ba, tabbas nan da shekara 10 ina tantamar zamu cigaba da kasancewa ƙasa ɗaya."

A wani labarin kuma Wayoyin wuta sun lantarke masu ibada ana tsaka da ayyukan Bauta a Lagos

Mutane sun shiga tashin hankali da bala'i a cocin El-Adonai Evangelical dake Abule-Egba jihar Lagos, lokacin da wayoyin wutar lantarki suka faɗo kan mutane ana tsaka da ibada.

Wani shaida, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya auku ne yayin da mambobin cocin ke kokarin gyara tuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel