Jerin mutanen da azumi ya fadi a kan su inji Malaman addini

Jerin mutanen da azumi ya fadi a kan su inji Malaman addini

A yayin da ake cikin tsakiyar Watan Azumi a fadin Duniya, mun kawo jerin wasu daga cikin mutanen da shari’a ta daukewa nauyin azumi saboda wasu dalilai. Malaman musulunci ne su ka bayyana wannan.

Daga cikin wadanda azumi ya fadi a kan su, kamar yadda Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana, akwai mutum 12:

1. Mace mai jinin al’ada (Haihuwa)

2. Mace mai jinin haihuwa (Biki)

Wadannan Mata za su rama azumin da ake bin su bayan sun gama jini. Za a rama wannan azumi kafin zagoyawar shekara har a sake risker Watan na Ramadan

3. Matafiyi

4. Maras lafiya

Wanda yake kan hanyar tafiya yana iya shan azumi idan ya fahimci cewa zai jikkata a hanya. Haka zalika mai jinya wanda ciwon sa ke fuskantar barazana da azumi, zai iya hakura sai daga baya sannan ya rama.

5. Mai shayarwa (renon jariri)

6. Mai ciki (juna-biyu)

KU KARANTA: Manyan abubuwan da ya kamata mai azumi ya kiyaye a Ramadan

Mace mai dauke da ciki ko kuma wanda ke bada nono za ta iya hakura da azumi a cikin Watan Ramadan, idan har za su sha wahala. Za su rama azumin daga baya idan sun samu sarari ko kuma su ciyar.

7. Tsoho

8. Tsohuwa

Malamai sun ce idan tsufa ya iske mutum har ta kai ba zai iya azumi ba, shari’a ta dauke nauyi a kansa, daga baya wadannan Bayin Allah za su ciyar.

9. Mai larurar yunwa da kuma

10. Kishi

Wadanda su ke fama da rashin iya jurewa yunwa ko kuma kishin ruwa za su iya shan azumi, muddin an tabbatar da cewa za su samu matsala idan su ka cigaba da azumi. Wadannan za su ciyar a madadi.

11. Yaro

12. Mahaukaci

Hadisai sun nuna cewa babu alkalami a kan karamin yaro wanda bai balaga ba, haka kuma an dauke hukuncin shari’a a kan mahaukaci har sai sa’ilin da ya warke, don haka babu azumi a kan su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel