Tsohon Janar Ya ba Gwamnati Sinadarin Kawo Karshen Ta'addanci a Arewa
- Tsohon Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soja, Manjo-Janar Sani Kukasheka Usman (mai ritaya), ya fadi yadda za a magance rashin tsaro
- Ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin tsaro da aka gudanar a Kaduna da zummar gano yadda za a warware matsalar
- Birgediya Janar Kukasheka (rtd) ya ce ana bukatar abubuwa biyu, ciki har da sake fasalin yadda ake gudanar da tsarin soji a Arewa maso Yamma
Jihar Kadua — Tsohon Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soja, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman (rtd), ya bukaci a sake duba dabarun tsaro a yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.
Ya bayyana cewa hakan na da matuƙar muhimmanci domin magance matsalolin tsaro da suka addabi jihohin yankin, musamman Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Katsina.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Kukasheka ya yi wannan bayani ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar.

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya yi albashir ga Arewa kan matsalar ta'addanci, ya tabo alaka da Nijar
Sanarwar ta ce Kukasheka ya gabatar da wannan shawara ne yayin wani taron kwanaki biyu da aka gudanar a Kaduna, wanda ya haɗa jami’an gwamnatin Jihar Katsina da kwararrun tsaro.
‘Yadda za a magance ta’addanci,” in ji Kukasheka
Premium Times ta ruwaito Birgediya Janar Kukasheka ya yi takaicin yadda jihohi kamar Katsina ke fuskantar matsaloli kamar hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane.

Source: UGC
Ya nanata cewa waɗannan matsaloli babbar barazana ne ga shugabanci, ci gaban tattalin arziki da zaman lafiyar al’umma.
Ya ce:
“Magance waɗannan matsaloli yana buƙatar haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro, shirin samar da zaman lafiya da kuma dabarun shawo kan rikice-rikice.”
Kukasheka ya bayyana sinadarin magance ta’addanci
Kukasheka ya jaddada cewa magance matsalar tsaro ba wai kawai ya ta’allaka ne da amfani da sojoji ba, yana buƙatar ingantaccen shugabanci.
Daga cikin abubuwan da ya lissafa cewa za a bukata, akwai samar da ayyukan yi domin ci gavab matasa da kuma samun haɗin gwiwar al’umma gaba ɗaya.
Tsohon soja ya yabawa Katsina kan yaki da ta’addanci
Tsohon jami'in tsaron ya yabawa Gwamna Dikko Umaru Radda bisa matakan tsaro da ya ɗauka, ciki har da ƙirƙirar rundunar tsaron al’umma.

Kara karanta wannan
Ni ba Ba-Yarbe bane: IBB ya fadi gaskiyar karin sunan 'Babangida' a cikin sunansa
Haka kuma ya ce samar da ma’aikatar harkokin tsaro na cikin gida a ihar zai kara dakile matsalar, tare da ba da shawarar a kara neman hadin gwiwar masana.
Yaki da ta'adadnci: Amurka za ta taimaki Najeriya
A baya, kun ji cewa Shugaban rundunar sojin saman Amurka a Turai da Afrika, Janar James Hecker, ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da kai hare-hare kan kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Janar Hecker ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi yayin taron hafsoshin sojin saman Afirka, inda ya ce barazanar ‘yan ta’adda tana shafar Afrika da kuma Amurka.
A cewar Janar Hecker, hare-haren da Amurka ke kaiwa sun hada da farmaki kan kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar ISIS da Boko Haram, wadanda ke barazana ga zaman lafiyar nahiyar Afrika.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng