'Yan Sanda Sun Samu Galaba kan 'Yan Ta'adda, Sun Tura Miyagu zuwa Lahira

'Yan Sanda Sun Samu Galaba kan 'Yan Ta'adda, Sun Tura Miyagu zuwa Lahira

  • Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan
  • Ƴan sandan sun hallaka wasu ƴan ta'adda guda huɗu a jihar Ƙebbi bayan sun kai hari a wani ƙauye inda suka sace wani mutum ɗaya
  • Jami'an tsaron sun kuma fafata da ƴan ta'addan IPOB/ESN a yankin Kudu maso Gabas, inda suka tura da yawa daga cikinsu zuwa barzahu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara kan ƴan ta'adda a faɗin ƙasar nan.

Jami'an ƴan sandan sun kashe ƴan ta'adda tara tare da ƙwato bindigogi 23 da alburusai iri-iri a wasu hare-hare da suka kai a sassan ƙasar nan.

'Yan sanda sun hallaka 'yan ta'adda
'Yan sanda sun kashe 'yan ta'adda Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, a shafin X na rundunar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun nuna kwarewa, sun cafke mambobin Boko Haram a cikin gari

Ƴan sanda sun hallaka ƴan ta'adda

Kakakin ya bayyana cewa waɗannan hare-hare suna daga cikin ƙoƙarin rushe ƙungiyoyin ƴan ta'adda da kuma inganta tsaro a ƙasar nan.

Sanarwar ta nuna cewa a ranar 14 ga watan Fabrairu, 2025, wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Gobiraje da ke ƙaramar hukumar Suru a jihar Kebbi, inda suka sace wani mutum mai shekaru 60 mai suna Umaru Bawa.

Jami'an ƴan sanda a jihar Kebbi sun bi sawun ƴan ta'addan zuwa dajin Tundafari da ke yankin Dakingari, inda suka yi artabu da su, suka kashe huɗu daga cikinsu, sannan suka cafke ɗaya ɗauke da raunin harbin bindiga.

Ƴan sandan sun ceto wanda aka sace ba tare da wani rauni ba, kuma sun ƙwato Naira miliyan uku da aka riga aka biya a matsayin kuɗin fansa.

Ƴan sanda sun fafata da ƴan ta'addan IPOB

"Haka zalika, a ranar 8 ga watan Fabrairu, 2025, jami'an ƴan sanda a jihar Imo tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun kai samame sansanin ƴan ta'adda na IPOB/ESN da ke Ezioha Mbaitolu, Umuele Umuaka, ƙaramar hukumar Njaba."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi raga raga da 'yan bindiga, sun ceto mutumin da suka sace

"An kashe manyan kwamandojin ESN guda biyu, kuma an ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai, manyan bindigogi guda 13, da ɗaruruwan alburusai."
"A ci gaba da wannan aiki, a ranar 9 ga watan Fabrairu, 2025, jami'an sun koma dajin Nkwukwo da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli, kusa da iyaka da dajin Ubachima a Awomama, ƙaramar hukumar Oru ta Yamma, jihar Imo, inda suka yi kicibus da wata tawagar ƴan ta'adda."
"A musayar wutar da aka yi, an kashe manyan kwamandojin ƴan ta'adda guda uku. An kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, kowace ɗauke da alburusai 36, babbar bindiga guda daya, adda guda daya, babura guda huɗu, da kuma wasu kayan tsafi."

- ACP Olumuyiwa Adejobi

Kakakin ƴan sandan ya ce waɗannan nasarorin sun nuna jajircewar rundunar ƴan sanda wajen yaƙi da ta'addanci da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya.

Ƴan sanda sun yi bajinta

Faisal Garba ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da ƴan sandan suka samu kan ƴan ta'addan babban abin farin ciki ne.

Ya yaba musu kan irin ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga bayan sun gwabza fada a Katsina

"Wannan aɓin farin ciki ne sosai. Ba ƙaramin daɗi nake.ji ba idan na ji cewa an kashe ƴan ta'adda. Muna musu fatan ci gaba da samun nasara."

- Faisal Garba

Ƴan sanda sun cafke ƴan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundujar ƴan sandan Najeriya sun samu nasarar cafke ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Gombe.

Ƴan sandan sun cafke ƴan ta'addan a wani otal bayan samun bayanan sirri kan ayyukan da suke gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng