"Na Cika Alƙawari," Gwamna Ya Rabawa Ƴan Dabar Siyasa da Matasa Miliyoyin Naira
- Gwamnatin Katsina a karkashin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta rabawa matasa da yan daba tallafin kudi domin su dogara da kansu
- Gwamna Dikko Radda ya ce gwamnatinsa ta ware Naira miliyan 252 domin rabawa matasa 1,016 tallafi a faɗin ƙananan hukumomi 34
- Wannan shiri dai na ƙarƙashin tsarin gina goben matasa da ci gabansu wanda ke gudana ƙarƙashin hukumar raya kammfanoni ta Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - An bai wa matasa 1,016, mafi yawansu ‘yan daban siyasa daga mazabu 361 a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina tallafin Naira miliyan 252 domin su zama masu dogaro da kai.
Shirin bayar da tallafin, wanda Hukumar Raya Kamfanoni ta Jihar Katsina (KASEDA) ke gudanarwa, yana karkashin, "Tsarin gina goben matasa da ci gaba."

Asali: Facebook
Gwamnatin Katsina ta kaddamar da shirin ne domin tsamo matasa daga harkar dabanci da dakile neman sadaka a ma’aikatun gwamnati, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan
"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da taron rabon tallafin ne a ranar Talata a Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Katsina.
Shugabannin hukumomi daban-daban a jihar, kamar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), ‘yan sanda, Hisbah, shugabannin addini da sarakuna sun halarci taron.
Gwamna Dikko ya rabawa matasa N252m
A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta ware Naira miliyan 252 don tallafawa wadannan matasa 1,016
A cewarsa, wannan tallafi da aka ba matasa ɗaya ne daga cikin alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe wanda a yanzu ya cika.
Daraktar Hukumar Raya Kamfanoni ta Katsina (KASEDA), A’isha Malumfashi, ta ce tana fatan cewa wannan shiri zai kawo sauyi mai kyau a rayuwar wadanda suka amfana.
Matasa na bukatar a tallafa masu a Katsina
Kwamishinan matasa da wasanni, Zakari Shargalle, tare da takwaransa na harkokin tsaro da al’amuran cikin gida, Nasiru Danmusa, sun bukaci a hada kai don inganta rayuwar matasan Katsina.

Kara karanta wannan
Masu koyo da haddar Kur'ani Mai Girma za su samu gata, Gwamnatin Kano ta faɗi shirinta
Nasiru Danmusa ya ce Najeriya na da jimillar mutane miliyan 237, kashi 41 cikin 100 suna tsakanin shekaru daya zuwa biyar, yayin da kashi 52 cikin 100 ke tsakanin shekaru 15 zuwa 65.
"Kashi 93 cikin 100 na mutanen Najeriya suna tsakanin shekaru 1 zuwa 65. Haka kuma, kashi 40 cikin 100 na mutanen kasar na rayuwa a cikin talauci.
"A Arewa, kashi 77.7 cikin 100 na mutane na rayuwa cikin talauci. Wannan ne dalilin da ya sa gwamnatin Gwamna Dikko Radda ke bullo da shirye-shiryen karfafa matasa," in ji shi.
Gwamnatin Katsina za ta sa ido a tallafin
A lokacin taron, Gwamna Dikko Radda ya gabatar da takardar kudin tallafin ga wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, maza uku da mata biyu.
Domin tabbatar da cewa an yi amfani da wannan tallafi yadda ya dace, an kafa tsauraran matakai don sanya ido kan matasan.
Gwamnati ta bayyana cewa duk wanda aka kama yana yawo a ofisoshin gwamnati ko ma’aikatun jihar yana neman sadaka, za a dauki matakin hukunta shi.
Za a ɗauki ma'aikatan lafiya a Katsina
Kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta fara shirye-shiryen ɗaukar sababbin ma'aikatan lafiya 300 bayan barazanar ƙungiyar NANNM.
Kwamishinan lafiya na Katsina, Musa Funtua ya ce gwamnati ta kira zama da ƙungiyar ma'aikatan lafiya watau NANNM domin duba buƙatunta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng