Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Gwamna Fubara da Wakilan Ogoni a Abuja
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sa labule da Gwama Siminalayi Fubara na Ribas da jagororin yankin Ogoni kan batun haƙo mai
- Manyan kusoshin gwamnatin tarayya da suks haɗa da Nuhu Ribadu, shugaban NNPCL Mele Kyari da ministoci sun halarci taron a Aso Villa
- Babu wata sanarwa a hukumance kan dalilin wannan taro amma ana hasashen ba zai rasa nasaba da batun tsaftace yankin Ogoni da dawo da haƙar ɗanyen mai ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa yanzu haka da Gwamna Sim Fubara na jihar Ribas da shugabannin Ogoniland a Aso Villa da ke Abuja.
Gwamna Fubara ya isa fadar shugaban ƙasa wurin taron tare da Sanata Lee Maeba da sauran tawagar wakilan yankin Ogoniland.

Asali: Twitter
Tawagar Gwamna Fubara da suka je Aso Villa
Vanguard ta rahoto cewa daga cikin wakilan da ke tare da gwamnan har da sanatoci kamar Magnus Abe, Olaka Nwogu, Cif Victor Giadom, da Cif Kenneth Kobani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran yan tawagar Fubara su ne Monsignor Pius Kii, Leedom Mitee, Sanata Bennett Birabi Barry, Mpigi, da kuma Joe Poroma.
Haka kuma a ɓangaren gwamnati, babban daraktan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya halarci taron tare da Ministan Muhalli, Balarabe Abba,
Ministoci da ƙusoshin gwamnati sun halarci zaman
Ƙusoshin gwamnati da aka hanga sun shiga wannan zama sun kunshi ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris da ministan ci gaban yankuna, Abubakar Momoh.
Kazalika, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, wanda ke takun saka da Fubara, shi ma ya halarci taron.
Bugu da ƙari, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya halarci wannan taro a Aso Villa yau Talata.
Dalilin ganawar Tinubu da wakilan Ogoni
Duk da cewa ba a bayyana ajandar taron ba, amma ana hasashen ba zai rasa nasaba da batun tsaftace yankin Ogoni da kuma batun sake hako mai a yankin ba.
Idan za a iya tunawa, gamayyar kungiyoyin farar hula sun bukaci gwamnatin tarayya ta ware Dala tiriliyan 1 domin tsaftace yankin Neja Delta da kuma biyan diyya na asarar da aka yi, kafin a dawo da hako danyen mai a Ogoniland.
Sun bayyana matsayarsu ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabannin ƙungiyoyin fararwn hula ciki har da CAPPA da HOMEF.
Sanarwar ta nuna damuwar mazauna yanin Ogoni bisa yunkurin gwamnatin Najeriya na ci gaba da. haƙo albarkatun man fetur a yankinsu.
Gamayyar kungiyoyin ta bayyana yunƙurin gwamnati a matsayin rashin adalci ga lafiyar muhallinsu, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Ana ganin wannan batu ne babbar ajendar da wannan taron na Shugaba Tinubu ya jagororin Ogoni zai maida hankali a kai.
Gwamna ya kaɗa hajjin yaran Wike
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Fubara ya jaddada cewa ba zai zuba ido yana kallon wasu tsiraru na neman maida shi baya ba.
A wani taron addu'o'i a coci, Siminalayi Fibara ya ce maƙiyan jihar Ribas ba za su yi nasara ba, za su ci gaba da shan kunya a idon duniya.
Asali: Legit.ng