TCN Ya Fadi Yadda ake Shirya Masa Makarkashiyar wajen Wadata 'Yan Najeriya da Wuta

TCN Ya Fadi Yadda ake Shirya Masa Makarkashiyar wajen Wadata 'Yan Najeriya da Wuta

  • TCN ta tabbatar da lalata tsofaffin turakun wuta guda 18 a wasu jihohi uku na kasar, wanda ke kawo babbar matsala
  • Kamfanin ya roki ‘yan Najeriya da su taimaka wajen kare kayan wutar lantarki domin amfaninsu da TCN
  • Jami'ar hulda da jama'a kamfanin ta ce masu sace-sacen kayan da masu sayen kayayyakin ba su kyauta wa ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa an lalata turakun wutar lantarki akalla guda 18 daga ranar 9 zuwa 14 ga watan Janairu, 2025.

Kamfanin, ta cikin sanarwar da ya fitar ya ce lamarin ya yi kamari ne a jihohin Kano, Ribas da Abuja, a lokacin da ya ke kokarin ganin hasken wutar lantarki ya wadata.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Lantarki
An lalata kayan wuta a jihohi 3 Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa mai magana da yawun kamfanin, Ndidi Mbah, ta fitar a ranar Lahadi, ta ce lalata kayayyakin wuta da ake ta fama da shi yana zama babbar matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TCN ya na neman hadin kan jama'a

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa TCN ta roki ‘yan Najeriya da su taimaka wajen kare kayan wutar lantarki domin amfaninsu da tsare hanyar samar masu da hasken wuta.

A cewarta, ya kamata kowa ya dauki tsarin wutar lantarki a matsayin dukiyar kasa wadda kowa ke da alhakin karewa, kuma hakan zai kara inganta rayuwar jama'ar kasa.

An lalata kayan wutar lantarki a Kano

TCN ta ce a Kano, masu lalata kayayyaki sun lalata turakun wuta na 105, 106, da 107 da ke kan layin Katsina-Gazoua mai karfin 132/33kV a ranar 9 Janairu, 2025

A ranar 17 Janairu, TCN ta sanar da wani hari da aka kai kan layin wutar lantarki da ke bai wa yankunan Abuja wuta, inda aka lalata wasu kayayyakin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

A watan Disamba, 2024, layin wuta mai karfin 330V na Shiroro-Katampe ya samu irin wannan hari daga masu lalata kayayyaki.

TCN ya soki masu sayen kayan sata

Ndidi Mbah ta ce masu lalata kayayyakin wutar lantarki da kuma masu sayen kayan da aka sata suna yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, tare da jefa al’umma cikin duhu.

Mbah ta ce Emmanuel Okpa, babban manajan sashen wutar lantarki na Fatakwal, ya ce masu sintiri sun gano an lalata turakun 171 zuwa 181 da kuma turaku na 184 a ranar 10 Janairu.

Ta ce an kai hari kan turakun 146, 147, da 149 a kan layin Owerri/Ahoada mai karfin 132kV a Ribas, inda aka cire ginshikan turakun, lamarin da ya kawo tangarda gare su.

TCN: An sace kayan wutar lantarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin wutar lantarki ya ce mazauna Abuja, har da wani sashe na fadar shugaban kasa za su shiga duhu bayan an sace kayan wutar.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi yadda aka zuba jarin $6.7bn a bangaren makamashi

Ndidi Mbah, jami'ar hulda da jama'a ta kamfanin ta ce lamarin zai kawo matsaloli a yankunan Maitama, Wuse, Jabi, Lifecamp, Asokoro, Utako, Mabushi, da sashen Fadar Shugaban Kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.