Tsautsayi Ya Ratsa Taron Ta’aziyyar Mahaifin Dan Majalisar Jiha a Katsina

Tsautsayi Ya Ratsa Taron Ta’aziyyar Mahaifin Dan Majalisar Jiha a Katsina

  • Ana zargin jami'an tsaron Katsina na 'Community Corps Watch' sun jikkata jama'a tare da hallaka mutum guda
  • Lamarin ya afku ne a lokacin da jami'an da ke cikin tawagar gwamna Dikko Umaru Radda su ka fara habe-harben isla
  • Gwamnan ya ziyarci garin Machika a karamar hukumar Sabuwa domin ta'aziyyar rasuwar mahaifin dan majalisar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - An tsinci labarin da ya girgiza al’umma a garin Machika na Karamar Hukumar Sabuwa, jihar Katsina, inda aka kashe Alhaji Sani Murtala.

Wanda aka kashe, siriki ne ga dan majalisar dokokin Katsina mai wakiltar Sabuwa, Hon. Ibrahim Danjuma Machika wanda ake zaman makokin mahaifinsa.

Katsina
An kashe sirikin dan majalisar Katsina a wajen ta'aziyya Hoto: @DanKatsina50
Asali: Facebook

Wani mai amfani da shafin X, Bakatsine, ya wallafa cewa lamarin ya faru ne yayin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ziyarci garin domin ta'aziyya ga dan majalisar.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa jama'a sun shiga firgici a lokacin da harsashi ya fara samun mutanen da ke zaune su na jimamin rasuwar mahaifin Hon. Ibrahim Danjuma Machika.

Yadda aka kashe sirikin dan majalisar Katsina

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami’an tsaron Katsina na "Community Watch Corps' da ke cikin tawagar rakiyar tsaron gwamnan sun fara harbin iska bayan isarsu wajen.

A lokacin ne aka samu rashin sa’a, daya daga cikin harsashin ya samu Alhaji Sani Murtala tare da wasu da ke zaune su na jimamin babbar rashin da aka yi wa Dan majalisar jihar.

Sirikin dan majalisar Katsina ya rasu

Alhaji Sani Murtala ya riga mu gidan gaskiya sakamakon raunukan da ya samu, yayin da sauran wadanda suka jikkata suke samun kulawar likitoci a halin yanzu.

Har yanzu ba a gano jami’in da ya yi harbin da ya yi sanadiyyar mutuwar ba, kuma rundunar ‘yan sandan Katsina ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida ya jawo hadimin Kwankwaso, ya nada shi a Mukami

Gwamnatin Katsina ta yi shiru a kan lamarin

Kawo lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar Katsina ba ta fitar da wani bayani a kan mummunan al'amarin da ya jawo asarar rai yayin ziyarar gwamna zuwa Machika ba.

Legit ta tuntubi rundunar yan sandan jihar, inda nan ma DSP Abubakar Sadiq bai amsa waya ba ko sakon da mu ka aika masa domin karin bayani a kan lamarin.

Lamarin dai ya dagawa jama'a hankali tare da jawo ce-ce-ku-ce tsakanin al’umma, inda ake kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci da daukar matakan da suka dace.

Harin yan ta'adda ya fusata gwamnatin Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Katsina, Umaru Radda Radda ya bayyana takaicin yadda 'yan bindiga su ke ci gaba da kai hare-hare a kan mazauna jihar.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun farmaki wasu ma’aikatan lafiya da ke kula da marasa lafiya a babban asibitin Kankara, inda suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Katsina ta hanyar kara inganta matakan tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.