Gwamnnatin Tinubu Ta Fadi Lokacin Fara ba Kananan Hukumomi Kudadensu Kai Tsaye
- Fadar shugaban ƙasa ta ba da tabbaci kan cin gashin kan ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar nan
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce daga watan Janairu za a fara tura musu kuɗaɗensu kai tsaye
- Ya buƙaci jama'a su karkatar da hankalinsu kan yadda jihohi da ƙananan hukumomi suke kashe kuɗaɗensu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana lokacin da za a fara ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye.
Fadar shugaban ƙasan ta bayyana cewa daga wannan watan na Janairu, ƙananan hukumomi a fadin ƙasar nan, za su fara karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun rarraba kuɗi na tarayya (FAAC).

Asali: Facebook
Hakan ya fito ne daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, yayin wata hira da ya yi da tashar Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunday Dare ya tabbatar da ƙudirin shugaba Bola Tinubu na aiwatar da hukuncin Kotun Koli, wanda aka yanke a watan Yulin 2024, kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Ƙananan hukumomi sun samu ƴanci
Kotun Koli ta yanke cewa ikon da jihohi suke yi kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi ya saɓawa kundin tsarin mulki.
Kotun Ƙolin ta yanke hukuncin cewa a riƙa biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye ko kuma ta hannun jihohi.
Sai dai, saboda matsalolin da ake samu idan suka bi ta hannun jihohi, kotun ta umarci a riƙa biyan kuɗaɗen kai tsaye ga ƙananan hukumomi.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da ministan sharia, Lateef Fagbemi (SAN), ya shigar domin tabbatar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi 774 na Najeriya.
Duk da cewa an yanke hukuncin a watan Yuli 2024, aiwatar da shi ya samu jinkiri domin tabbatar da cewa an samar da tsarin da ya dace.
Yaushe za a fara tura kuɗaɗen kananan hukumomi?
"Muna da shugaban ƙasa wanda ke tabbatar da cin gashin kan ƙananan hukumomi."
“Na yi magana da wani shugaban ƙaramar hukuma wanda ya tabbatar da cewa zai samu N2.9bn, maimakon N200m da yake samu a baya."
"Don haka daga ƙarshen wannan wata, za a fara biyan kuɗaɗen kai tsaye ga ƙananan hukumomi.”
- Sunday Dare
Sai dai, Sunday Dare ya jaddada buƙatar a ƙara sanya ido kan yadda jihohi da ƙananan hukumomi ke amfani da kuɗaɗen da suke samu.
"Wata jiha ta samu N499bn a bara, kusan ninki huɗu na kuɗin da ake ba ta a baya, amma babu wani abin arziƙi da aka yi da kuɗaɗen."
- Sunday Dare
Sunday Dare ya ce duk da cewa gwamnatin tarayya tana fuskantar suka akai-akai, akwai buƙatar hankalin jama’a ya karkata kan yadda jihohi da ƙananan hukumomi ke amfani da kuɗaɗen da ake ba su.
Muna fatan abin ya tabbata
Wani tsohon Kansila a jihar Katsina, Muhammad Lukman ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas talakawa za su ga canji idan aka fara ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye.
Ya bayyana cewa abin a yaba ne yadda Shugaba Bola Tinubu ya dage wajen ganin ƙananan hukumomi sun samu ƴancin cin gashin kansu.
"Muna fatan tsarin nan ya tabbata domin talakawa za su amfana sosai. Abin da shugaban ƙasan abin a yaba ne."
- Muhammad Lukman
Tinubu ya ba gwamnoni tabbaci
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kawar da fargabar da gwamnoni suke da ita kan ƴancin ƙananan hukumomi.
Shugaba Tinubu ya ba gwamnonin tabbacin cewa ko kaɗan ba ya da shirin karɓe iko a kan ƙananan hukumomi daga hannun shugabannin na jihohi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng