Bankin Duniya Ya Fitar da Sabon Hasashe a kan Tattalin Arzikin Najeriya

Bankin Duniya Ya Fitar da Sabon Hasashe a kan Tattalin Arzikin Najeriya

  • Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Najeriya zai samu ci gaba mai dorewa tsakanin 2025 da 2026 saboda sauye sauyen da aka samu
  • Daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Bola Tinubu ta fitar sun hada da cire tallafin man fetur da dokar haraji da ke gaban majalisa
  • Bankin ya bayyana cewa ana sa ran hauhawar farashi zai ragu, wanda zai karfafa saye da sayarwa da kara ci gaban tattalin arzikin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Bankin Duniya ya hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai samu matsakaicin ci gaban da 3.6% tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026.

Wannan hasashe na kunshe ne a cikin rahotonsa na Global Economic Prospects, wanda aka fitar a watan Janairu 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Tinubu
Bankin duniya ya ce tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Bankin ya danganta wannan ci gaba da ake samu da sauye-sauyen da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin manyan matakan da aka dauka har da cire tallafin mai a watan Mayun 2023 da kuma gyaran tsarin haraji da ke gaban majalisar dokoki ta kasa, wanda ya samu amincewar gwamnoni.

Bankin duniya ya yabi tsarin Bola Tinubu

Jaridar Punch rahoton ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta yi kwanan nan sun taimaka wajen karfafa kwarin gwiwar kasuwanci da inganta hanyoyin kudin shihga.

Rahoton Bankin Duniya ya ce:

"A Najeriya, ci gaban GDP ya karu zuwa 3.3% cikin a shekarar 2024 musamman a bangaren harkokin kudi da sadarwa. Gyaran tsarin tattalin arziki da kudin kasa sun taimaka wajen karfafa kwarin gwiwar kasuwanci."

Yadda bankin duniya ya yabi Najeriya

Bankin Duniya ya bayyana cewa matakan gyara na kudi da tsare-tsare sun rage gibin kasafin kudi sakamakon karin kudaden shiga da aka samu a kasar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Ya ce an yi nasarar ne bayan cire tallafin musayar kudi da tsarin sauya kudin kasashen waje, wanda ya haifar da karin kudaden shiga ga gwamnati, wanda zai habaka tattalin arziki.

Rahoton ya kara da cewa:

"Ana sa ran samun ci gaban tattalin arziki a yankin Afirka ta Kudu da yankin Sahara da 4.1% a 2025 da 4.3% a 2026, sakamakon sassauta yanayin kudi da kuma raguwar hauhawar farashi. Wannan ya sa hasashen ci gaba a 2025 da 2026 ya karu da 0.2% da 0.3%, bi da bi."

Bankin Duniya ya shawarci gwamnatin Tinubu

A baya kun ji cewa Bankin Duniya ya shawarci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan lamarin maido da tallafin man fetur, yana mai cewa matakin zai iya haifar da koma baya.

Wannan shawara ta fito ne a cikin wani rahoto na musamman da bankin ya fitar, inda ya bayyana tasirin cire tallafin man fetur da aka yi a watan Mayu na shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Rahoton ya bayyana cewa cire tallafin ya taimaka wajen kara kudin shiga na gwamnati da rage gibin kasafin kudi, sannan matakin ya bai wa gwamnati damar mayar da hankali kan wasu ayyukan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.