Sufeton 'Yan Sanda Ya Hargitsa Majalisa yayin Kare Kasafin Kudin 2025

Sufeton 'Yan Sanda Ya Hargitsa Majalisa yayin Kare Kasafin Kudin 2025

  • 'Yan majalisar tarayya sun samu sabani yayin da Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ke kare kasafin kudin shekarar 2025
  • Rahotanni sun nuna cewa rikici ya barke kan zargin cewa akwai takardun kasafin da ba su zo hannun 'yan majalisar dattawa ba kafin zaman
  • Egbetokun ya nemi karin kudi da tallafi domin karfafa aikin 'yan sanda, ciki har da karin adadin jami'ai daga 10,000 zuwa 30,000 a shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Taron majalisar tarayya ya dauki zafi yayin kare kasafin kudin shekarar 2025 da Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun ya gabatar.

A yayin gabatar da karin bayani kan kudin da aka ware domin gina hedikwatocin 'yan sanda a yankuna, rikici ya barke tsakanin 'yan majalisar dattawa da na wakilai.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

IGP Kayode
Yadda aka samu rudani a zaman kare kasafin 'yan sanda. Hoto: Bayo Onanuga|Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa wasu 'yan majalisa sun koka kan rashin samun cikakken bayani kan kasafin kudin da Kayode Egbetokun ke gabatarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin da ya barke a lokacin kare kasafin kudi

Rikicin ya fara ne yayin da wani dan majalisa daga Akwa Ibom, Mark Esset ya dakatar da IGP Egbetokun daga bayani, yana mai tambayar dalilin rashin dacewar takardun da aka raba.

Hakan ya jawo takaddama tsakanin 'yan majalisar, musamman lokacin da Sanata Onyekachi Nwebonyi daga Ebonyi ya nemi takardun kasafin domin tabbatar da gaskiyar bayanan sufeton.

Sanata Nwebonyi ya bayyana cewa;

“Mun taru a nan ne domin yi wa 'yan Najeriya aiki, kuma suna kallonmu a matsayin masu muhimmanci. Ya dace mu samu dukkan bayanai da ake tattaunawa a kansu.”

Martanin kwamitin harkokin 'yan sanda

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin 'Yan Sanda, Abubakar Yalleman, ya yi watsi da batun Sanata Nwebonyi, ya bayar da damar cigaba da gabatar da kasafin.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

Sanata Nwebonyi ya fusata ya tattara kayansa ya bar zaman, inda ya shiga muhawara mai zafi da wasu 'yan majalisar wakilai kafin ya fice.

Dan Majalisar Wakilai, Yusuf Gagdi daga Jihar Filato, ya bayyana rashin jin dadinsa kan rikicin, yana mai cewa ba daidai ba ne dan majalisa ya yi jawabi yayin da ba shi da damar magana.

Kira kan kara tallafawa 'yan sanda

Bayan an shawo kan matsalar, IGP Egbetokun ya ci gaba da gabatar da jawabi, yana mai bayyana bukatar karin kudi ga 'yan sanda domin inganta ayyukansu.

Ya kuma nemi a daina amfani da tsarin kasafin da suke kai yana mai cewa tsarin yana hana samun kudin da suka dace domin gudanar da ayyukan tsaro.

Sufeto Janar ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya karawa rundunar adadin wadanda ake dauka aiki daga 10,000 zuwa 30,000 a shekara. Ya ce matakin zai kara inganta ayyukansu.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Bukatar taimako daga majalisa

The Cable ta wallafa cewa IGP Egbetokun ya roki 'yan majalisar su taimaka wa rundunar wajen samun isasshen tallafi da kayan aiki domin inganta aikinsu na tsaro.

Ya yaba wa kwamitin da ya fahimci karancin kudin da rundunar 'yan sanda ke fuskanta, yana mai cewa suna fata za a samar da karin tallafi domin saukaka matsalolin tsaro a kasar nan.

An tono masu taimakon Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa tsofaffin jami'an tsaron Najeriya sun yi magana kan yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa.

Legit ta rahoto cewa jami'an sun zargi kungiyoyin sa-kai da tallafawa 'yan Boko Haram da 'yan ta'adda da makamai wajen yin ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng