Alkali da Lauyoyi Sun Tsure yayin da Aka Fara Harbe Harbe ana tsaka da Shari'a a Kotu

Alkali da Lauyoyi Sun Tsure yayin da Aka Fara Harbe Harbe ana tsaka da Shari'a a Kotu

  • Ƙarar harbe-harbe ya tada hankula a kotun sauraron ƙorafe-ƙotafen zaben gwamnan Edo ranar Laraba, 15 ga watan Janairu, 2025
  • An ruwaito cewa jami'an tsaro sun kai ɗauki kotun cikin sauri wanda ya ba da damar ci da sauraron kararrakin da jam'iyyu bakwai suka shigar
  • Shugaban APC na Edo, Jarret Tenebe, ya yi tir da harbe-harben, yana bayyana su a matsayin barazana ga adalci da tsaron mutane

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - An ji harbe-harbe a safiyar Laraba a kusa da wurin zaman Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar Edo da ke birnin Benin.

Hankula mutanen da ke cikin kotun sun tashi sakamakon jin karar harbe-harben bindiga ana tsaka da zaman shari'a karkashin jagorancin Mai Shari’a Wilfred Kpochi.

Taswirar Edo.
Karar harbe-harbe ya tada hankula a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Likitoci, ‘yan siyasa, lauyoyi da manema labarai sun yi kokarin tserewa don kaucewa harbin alburushi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

ICPC ta sake cafko wani mutumin El Rufa'i, za a tafi kotu da shi kan zargin rashawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun kai ɗauki a kan lokaci

Sai dai zuwan jami’an tsaro dauke da makamai kuma cikin shirin ko ta kwana ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

An tattaro cewa zuwan dakarun ya ba da damar ci gaba da shari'a kan zaɓen gwamnan a kotun da ke zamanta haɗabar babbar kotun Edo da ke kan titin Sapele a Benin.

Shugaban jam’iyyar APC ta Edo, Jarret Tenebe, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana bayyana harbe-harben a matsayin abin damuwa da ba za su lamurta ba.

Shugaban APC ya yi tir da harbe-harben

Tenebe ya ce:

“Kotun zaɓe wuri ne mai muhimmanci da ake gudanar da shari’a cikin adalci, duk wani abu da zai kawo tashin hankali a cikinta yana lalata tsarin shari’armu, kuma yana barazana ga lafiyar duk wanda abin ya shafa.”
"Duk da bambancin ra'ayi na siyasa, amfani da tashin hankali don warware rikice-rikice ba zai taɓa zama alheri ba. Dole ne mu yi Allah-wadai da wannan harbe-harbe da kakkausar murya."

Kara karanta wannan

Rikici ya sake kacamewa a PDP, sabon shugaban jam'iyya ya bayyana

Shugaban APC na Edo ya ƙara da cewa tayar da zaune tsaye ba shi da wuri, yana mai bayyana cewa ya zama dole a hukunta waɗanda suka aikata hakan.

Jam'iyyu 7 suka shigar da ƙara kotun zaɓe

Sanata Monday Okpebholo, tsohon Sanatan Edo ta Tsakiya a Majalisar Dattawa kuma ɗan takarar APC ne ya lashe zaɓen gwamna na ranar 21 ga Satumba, 2024.

Okpebholo ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Edo ranar 12 ga Nuwamba, bara.

Daga cikin jam'iyyun siyasa 18 da suka fafata a zaɓen, guda bakwai sun shigar da ƙorafi a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Jam'iyyun da suka kai kara sun haɗa da PDP, SDP, ZLP, ADP, Accord, APM, da kuma AA.

Kusan kowace jam'iyya daga cikinsu ta nemi kotun zaɓen ta soke zaɓen Gwamna Okpebholo tare da ayyana ɗan takararta a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓe.

Kara karanta wannan

'Dalibai sun yi wa mataimakiyar gwamna rubdugu da sanduna, ta sha da ƙyar

Rikici ya ɓarke bayan tsige ciyaman a Edo

A wani labarin, kun ji cewa rikici ya ɓarke a jihar Edo kan tsige shugabannin ƙananan hukumomin da aka yi wanda ake zargin da sa hannun sabon gwamna.

Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun jikkata a ƙaramar hukumar Uhunmwonde a harin da wasu tsageru suka kai bayan tsige ciyaman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262