An Samu Asarar Rayuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota, Mutum 60 Sun Jikkata

An Samu Asarar Rayuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota, Mutum 60 Sun Jikkata

  • An shiga jimami a jihar Kogi bayan an samu aukuwar wani hatsarin mota a babban birnin Lokoja a ranar Talata, 14 ga watan Janairun 2025
  • Hatsarin motan wanda ya auku bayan wata babbar motar ɗaukar kaya ta. Ƙwacewa direbanta ya jawo asarar rayukan mutum shida
  • Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Kogi ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya yi kira ga direbobi da su riƙa bin dokokin tuƙi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a birnin Lokoja na jihar Kogi.

Hatsarin motan wanda ya auku a birnin Lokoja ya yi sanadiyyar rasuwar mutane shida yayin da wasu mutum 60 suka jikkata.

Motoci sun yi hatsari a Kogi
Mutum shida sun rasu a hatsarin mota a Kogi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Punch ta rahoto cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana a ranar Talata, a kusa da shateletalen Zone 8, kan titin Hassan Katsina a birnin Lokoja.

Kara karanta wannan

Ana shirin ƙara farashin fetur a Najeriya, NNPCL ya tara wa gwamnati Naira tiriliyan 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar FRSC ta tabbatar da aukuwar lamarin

Shugaban hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kogi, Samuel Oyedeji, ya tabbatar da aukuwar lamarin, cewar rahoton tashar Channels tv.

Samuel Oyedeji ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne bayan wata babbar motar ɗaukar kaya ta ƙwace.

Shugaban na FRSC ya yi kira ga direbobi musamman masu tuƙa manyan motoci da su yi taka-tsan-tsan, tare da yin kira ga gwamnati da ta ƙara ƙoƙari wajen gyaran tituna da kuma tilasta bin dokokin hanya.

"Wata babbar mota mai ɗaukar kaya da ke tafiya daga Bauchi zuwa jihar Enugu ta ƙwacewa direbanta, wanda hakan ya haifar da mummunan hatsari."
"An ajiye gawarwakin mutane shida da suka rasu a dakin ajiye gawa na Asibitin koyarwa na jami’ar tarayya."
"A yayin da bincike ke ci gaba domin gano musabbabin hatsarin, ana tunatar da ƴan Najeriya game da muhimmancin tabbatar da bin ƙa'idojin tuƙi domin amfanin kowa.

Kara karanta wannan

ICPC ta sake cafko wani mutumin El Rufa'i, za a tafi kotu da shi kan zargin rashawa

- Samuel Oyedeji

Hatsarin mota ya yi ɓarna a jihar Kogi

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa lamarin ya haifar da tashin hankali.

"Abin ya ba ni tsoro sosai. Mutane sun maƙale a cikin motoci, kuma an ɗauki sa’o’i kafin a iya gyara wurin."

- Wani ganau

Wannan mummunan lamari ya sake jaddada bukatar tabbatar da dokoki masu tsauri kan hanyoyin da direbobi ke amfani da su, da kuma tabbatar da lafiyar motocin dake tafiya don rage yawan asarar rayuka a titunan Najeriya.

Hatsarin mota ya ritsa da ƴan ɗaurin aure

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mutanen Kano da suka je ɗaurin aure a jijar Plateau sun gamu da wani mummunan hatsari.

Hatsarin wanda ya auku Kwanar Maciji a ƙaramar hukumar Pankshin ta jihar Plateau, ya yi sandiyyar rasuwar mutane 19 har lahira.

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen Plateau ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ƙara da cewa wasu mutum 11 sun jikkata, yayin da suke dawowa daga halartar ɗaurin auren.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng