Bayan Shafe Shekaru 99 a Duniya, Tanko Yakasai Ya Fadi Babban Burinsa ga Najeriya

Bayan Shafe Shekaru 99 a Duniya, Tanko Yakasai Ya Fadi Babban Burinsa ga Najeriya

  • Ɗaya daga cikin mutanen da su ka karɓo ƴancin Najeriya daga turawan mulkin mallaka ya fadi fatansa ga ƙasar
  • Alhaji Tanko Yakasai ya yi wannan bayani ne bayan shafe shekaru 99 a duniya inda ya jima wajen hidimtawa ƙasa
  • Ya bayyana fatan Najeriya ta dunƙule a matsayin ƙasa guda mai cike da albarka da ci gaba da zai ratsa dukkanin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Dattijo a Arewa kuma guda daga cikin waɗanda aka yi fafutukar samun ƴancin ƙasa da su, Alhaji Tanko Yakasai ya faɗi burin da ya ke da shi.

Ya bayyana haka ne a a lokacin da ya cika shekaru 99 a duniya da shafe tsawon shekaru ana gwagwarmayar saita siyasar ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

Yakasai
Tanko Yakasai ya yi fatan ci gaban Najeriya Hoto: Deji Adeyanju
Asali: Facebook

A labarin da ya kebanta ga jaridar The Sun ta wallafa cewa, Alhaji Tanko Yakasai ya gode wa ƴan ƙasar nan bisa taya shi murnar ganin shekaru 99 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Burin Tanko Yakasai ga ƙasar nan

Alhaji Tanko Yakasai ya ce ba shi da burin da ya wuce ganin kasar na ta dawwama a cikin haɗin kai da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Dattijon ya ƙara da fatan Najeriya za ta zamo ƙasa inda zaman lafiya, adalci, da wadata za su tabbatu ga dukkanin ƴan ƙasa.

“Ina fatan wannan ƙasa za ta ci gaba da wanzuwa a cikin zaman lafiya da haɗin kai, kuma ta ci gaba da jin daɗin ‘yancin da muka yi fafutuka samo wa."

Ra'ayin Yakasai kan salon mulkin Najeriya

Alhaji Tanko yakasai ya ce babu laifi a tsarin mulkin shugabancin irin na Amurka da ake amfani da shi a halin yanzu a Najeriya. Ya na ganin 'yan kasa na da damar gwada wani tsarin mulki idan sun gamsu cewa tsarin da ake amfani da shi yanzu ba ya haifar da ɗa mai ido.

Kara karanta wannan

An gano dalilin wasu ƴan Najeriya na baƙin ciki da farfaɗowar Naira

Yakasai ya faɗi ra'ayinsa kan raba ƙasa

A baya, mun ruwaito cewa dattijo a Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana rashin dacewar kiraye-kirayen da wasu ke yi na buƙatar a raba Najeriya zuwa ƙasashe daban-daban.

Ya bayyana wa Legit cewa mutanen da ke irin waɗannan kiraye-kiraye ba su san me su ke fatan ta tabbata ga kasar ba, inda ya shawarci jama'a a yi aiki tare don samun cigaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.