Daga Karshe, NNPCL Ya 'Sanar' da Farashin Man Fetur a Matatar Fatakwal
- Kungiyar PETROAN ta bayyana cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya sanar da farashin fetur daga Fatakwal
- A sanarwar da kungiyar dillalan man fetur ta fitar, ta nemi NNPCL ta sassauta farashi saboda bikin kirsimeti
- PETROAN ta kara da cewa har yanzu kofarta a bude ta ke ga sauran matatun fetur da ake da su a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Kungiyar dillalan man fetur (PETROAN) ta bayyana cewa kamfanin NNPCL ya yanke farashin da zai sayar masa da fetur da aka tace a matatar Fatakwal.
Wannan na zuwa ne bayan kungiyar PETROAN ta ce ta na jiran a sanar da farashin fetur na matatar da aka gyara a hukumance.
Jaridar Punch ta wallafa cewa kamfanin NNPCL ya ce matatar Fatakwal za ta sayar da litar man fetur a kan N1,030 ga yan kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya fara karbar kudin kayan matatar Fatakwal
Jaridar The Daily Post ta wallafa cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL), ya sanar da fara karbar oda daga masu bukatar fetur daga matatar Fatakwal.
Mai magana da yawun PETROAN na kasa, Joseph Obele, ya ce;
“Kamfanin NNPCL ya sanar da mu cewa farashin PMS a matatar Fatakwal shine N1,030 a kowace lita. Haka kuma an sanar da PETROAN cewa an bude shafin neman kaya don yin oda.”
PETROAN ta nemi NNPCL ya rage farashin mai
Dillalan man fetur karkashin kungiyar PETROAN sun bukaci kamfanin NNPCL ya duba yadda farashin fetur daga matatarsa na NNPCL da zummar yin ragi.
Jami'in hulda da jama'a na kungiyar na ganin idan aka samu ragin farashin, zai ba masu bikin kirsimeti damar gudanar da shagulgula a cikin walwala.
PETROAN ta fadi yadda ta sayi man fetur
A baya, mun ruwaito kungiyar dillalan man fetur a inuwar PETROAN ta musanta cewa ta sayi fetur daga kamfanin NNPCL a kan sabon farashi bayan gyara matatar Fatakwal.
Shugaban PETROAN na kasa, Dakta Billy Sotubo, ya shaida cewa fetur din da su ka saya a baya-bayan nan ya zo masu a kan tsohon farashi, amma su na sa ran a fitar da sabon farashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng