Kin Taba Yi a Gidanku? Jama’a Sun Taso Budurwar da Ta Yi Wanke-Wanke a Gidan Su Saurayinta a Gaba
- Wata kyakkyawar buduwar ya kai ziyara gidan su saurayin da za ta aura, ta sha aikin wanke-wanke da aika
- A wani bidiyon da aka yada, an ga budurwar a lokacin da take tikar aiki a gidan su saurayin, ta yi wanke-wanke da wanki
- Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun bayyana ra’yoyinsu kan yadda budurwar ta kai wannan ziyarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wata budurwa ‘yar Najeriya ta jawo magana kafar sada zumunta yayin da ta kai ziyara gidan surukanta ta taya su aiki.
A lokacin da ta kai ziyarar, an tara mata ayyukan gida, inda aka ce ta wanke kwanukan abinci.
A cikin bidiyon da aka yada, an ga lokacin da budurwar ta tafi aika da surukanta suka ba ta. An kuma ga lokacin da take wanke madafa.

Asali: TikTok
Yadda aka tara mata wanke-wanke
Wani rusheshen likidiri da aka tara kwanukan wanke-wanke da aka tara mata ya dagawa mutane hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta yada bidiyin ne a shafinta na TikTok @soniameyson don jin ra’ayin jama’a ko sun taba fuskantar irin wannan lamarin.
Kalli bidiyon a nan:
Ga martanin jama’a a kasan bidiyon da ta yada:
Omotolani29:
“Watakila ta gabatar da kanta a matsayin ‘yar wanke-wanke ne, don ni dai ban gane ba.”
somtochukwu:
“Kada ki fara abin da ba za ki iya karasawa ba.”
Ayotomiwa:
“Meye zan yi a madafa, ni fa bakuwa ce.”
Debbie:
“Shin ba su wanke gidan ne da?? Meye yasa za ki tiki wannan aikin daga zuwa?? Ko dai ke kika zabi taimaka masu?”
toun:
“Tambaya ita ce, shin an muku baiko da wannan mutumin?”
Tessy Cosmas:
“Shin kin taba irin wannan aikin a gidan iyayenki?”
Margaret:
“’Yar uwar tsohon saurayina ta taba cewa na mata wanke-wanke, nace zan dauka mata ‘yar aiki.”
lekwaamarachi:
“Baki wanke kofar gidan ba ‘yar uwa.”
Mai sana'ar wanke-wanke a Turai ya magantu
A bangare guda, wani dan kasar Ghana mazaunin Jamus ya bayyana karin haske game da sana’ar da yake ta wanke-wanke a kasar Turai, ya girgiza jama’ar intanet.
Da yake zantawa da wata tashar YouTube, Kofi Asiedu y ace yana samun akalla £1,920 (N1,060,582.08) duk wata daga sana’ar wanke-wanke.
Asiedu ya yi fashin bakin kudin da yake samu duk sa’a daya, duk rana ta Allah, duk mako da kuma wata a kasar.
Asali: Legit.ng