Mai Sana’ar Wanke-Wanke a Turai da Ke Samun Sama da N1m Ya Gitgiza Jama’a a Intanet

Mai Sana’ar Wanke-Wanke a Turai da Ke Samun Sama da N1m Ya Gitgiza Jama’a a Intanet

  • Wani dan kasar Ghana da ke zaune a Jamus ya yi karin haske game da aikin da yake na wanke-wanke a kasar ta Turai
  • A wata hira da aka yi dashi, Kofi Asiedu ya bayyana irin tagomashin da yake samu daga kama sana’ar wanke-wanke
  • Labarin wannan bawan Allah dai bai tsaya nan ba, mutane da yawa sun yaba masa bisa jajircewa da kuma kin raina sana’a

Wani dan kasar Ghana mazaunin Jamus ya bayyana karin haske game da sana’ar da yake ta wanke-wanke a kasar Turai, ya girgiza jama’ar intanet.

Da yake zantawa da wata tashar YouTube, Kofi Asiedu y ace yana samun akalla £1,920 (N1,060,582.08) duk wata daga sana’ar wanke-wanke.

Mai wanke-wanke da ke samun sama da N1m a wata
Mai Sana’ar Wanke-Wanke a Turai da Ke Samun Sama da N1m Ya Gitgiza Jama’a a Intanet | @Zionfelix TV/YouTube
Asali: UGC

Yadda aikin yake a Jamus

Asiedu ya yi fashin bakin kudin da yake samu duk sa’a daya, duk rana ta Allah, duk mako da kuma wata a kasar.

Kara karanta wannan

Ba zan taba fashi ba: Shigan da malamar aji ta yi ya girgiza dalibai, jama'a sun yi martani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Murjejen mutumin ya bayyana cewa, yakan samu £12 a duk sa’a daya, kuma yakan yi aikin sa’o’I takwas ne kacal a rana na tsawon kwanaki 5 a mako.

Sai dai, y ace kada mutane su yaudaru da yawan kudin, domin a cewarsa, wanke-wanke sana’a ce da ke bukatar natsuwa da kwarewa har ma da juriya.

Waka daga bakin mai ita

A cewarsa:

“Za ta tsaya ne kyam a kan kafafunka na sa’o’I 8. Za ka huta ne kawai na ‘yan mintuna 10 zuwa 20
“A nan ba z aka zo kana aiki kana wani abu ba misa kamar hawa shafukan sada zumunta. Mai gidanka ba zai bari ba.”

Asiedu ya shawarci dangin masu aiki a kasashen waje da su yi amfani da kudaden da ake tura musu wajen yin abu mai amfani da zai dawwama a nan gaba.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Matshi Da Yaje Ba Haya A Dawa Karke Da Fada Da Damisa Wadda Ta Jikkatashi

Ya kara da cewa, kudin ba wai da sauki ake samunsu ba, kawai dai da ke akwai ayyukan ne a kasar shi yasa hakan ke da sauki ga wasu.

Kalli bidiyon hirarsa:

Martanin ‘yan soshiyal midiya

Jama’a a kafar sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu game da ikrari da aikin da Asiedu yake yi a kasar Jamus, ga kadan daga abin da suke cewa:

Dan Jean:

“Ina taya shi murna da yake ba da labarin…Wasu bas a fadin maganar ma irin haka.”

David Cobbinah:

“Abin na fahimta daga wannan mutumin shine, yana da kankan da kai…saboda irin wannan aikin yana bukatar kankan da kai…idan baka da kankan da kai ba z aka iya yin irin wannan aikin ba.”

Cooking with Efya:

“…Ina ga babu wanda zai yi irin wannan aikin idan ba wai don rashin zabi ba hmmm!”

Ba wannan ne karon farko da ake samun maza na sana'ar wanke-wanke ba, an samu a baya, lamarin ya ba da mamaki.

Kara karanta wannan

Shahararren Mawakin Najeriya Zai Daina Waka, Zai Zama Makarancin Kur’anin Duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel