Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Bayan Mahaifiyarsa Ta Saka Ta Yin Wanke-wanke
- Lokacin haduwa da iyayen saurayi ya kan zo da tarin farin ciki a bangaren yan mata da dama, sai dai Bolladeasy 'yar kasar Indonesiya tana ganin nata ya zo da bautuwa
- A cewar matashiyar mai amfani da TikTok, da farko ta taimaka mata a kicin sannan bayan ta gama, sai da ta yi wanke-wanke
- Ta ce sam ba ta yi sannan nan take ta kawo karshen soyayyarsu tana mai cewa ta hango yadda kasancewa surukar dattijuwar matar zai zamo
Indonesiya - Wata matashiyar budurwa 'yar kasar Indonesiya ta rabu da saurayinta bayan mahaifiyarsa ta saka ta wanke tulin kwanonin da aka ajiye a kicin.
Belladeasy ta ki yin wanke-wanke
A ranar 25 ga watan Nuwamba, matashiyar mai suna Belladeasy a TikTok ta ce tana ta sa ran dattijuwar matar za ta ce mata kawai "tafi ki bar kwanonin a kan tebur."
Ba ta yi na'am da wannan bukatar ba, musamman ganin cewa ta rigada ta taimaka mata a kicin bayan mai shirin zama uwar mijin tata ta tambayeta ko ta iya girki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar matashiyar, haduwarta da iyayen saurayin ya zo da bautuwa sosai.
Bai zo da mamaki ba cewa Belladeasy ta dauki matakin gaggawa game da soyayyarta domin "ta hango yadda kasancewa surukar dattijuwar matar zai kasance.
"Oh Allah na, nagode maka."
Wasu jama'a basu yi na'am da matakin da Belladeasy ta dauka ba
A sashin sharhi, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu.
"Ba za mu iya zaban iyayenmu ba amma muna iya zaban surukanmu," cewar wata da ta yarda da matakin da Belladeasy ta dauka.
Wasu na ikirarin cewa bai kamata matar da dauki irin wannan tsattsauran mataki ba.
"Ki dara yanzu. Ki koka daga baya," in ji wata mai amfani da TikTok.
Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta tsallake, Ta Tare Da Mijinta a Turai, Sun Bar Jama'a Baki Bude
"A lokacin da na yi abun da uwar mijina ta bukaci na yi...ba a samu matsala ba ko kadan," cewar wata.
Budurwa ta fada son wani boka, har sun yi aurensu
A wani labari na daban, mun ji cewa wata budurwa ta cika da farin ciki yayin da ta garzaya soshiyal midiya don nunawa duniya masoyinta wanda ya kasance boka ne.
Asali: Legit.ng