‘Ta Kone Kurmus,’ Matashi Ya Babbaka Kakarsa Mai Shekaru 60 da Fetur

‘Ta Kone Kurmus,’ Matashi Ya Babbaka Kakarsa Mai Shekaru 60 da Fetur

  • Rundunar yan sanda Najeriya a jihar Jigawa ta cafke wani matashi da ake zargi da kona kakarsa bayan ya zuba mata man fetur
  • Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Sule Tankarkar amma yan sanda sun dauko matashin zuwa Dutse domin bincike
  • Matashin mai suna Nura Mas'ud ya bayyanawa yan sanda cewa ya gargadi kakarsa kan yawan magana da take a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Rundunar yan sanda ta kama wani matashi mai suna Nura Mas'ud da zargin bankawa kakarsa wuta.

Rahotanni na nuni da cewa an kama Nura Mas'ud ne a a ƙauyen Mua'azu a karamar hukumar Sule Tankarkar.

Kara karanta wannan

An shiga rudani da yan bindiga suka hallaka dan takarar APC, ana daf da zaɓe

Jigawa
Matashi ya kashe kakarsa a Jigawa. Hoto: Shiisu Adam Lawal
Asali: Facebook

Kakakin yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ne ya bayyanawa Legit yadda lamarin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya babbaka kakarsa a Jigawa

Rundunar yan sanda ta cafke wani matashi, Nura Mas'ud bisa zargin kashe kakarsa ta hanyar ƙona ta.

Ana zargin Nura mai shekaru 26 ya kona Zuwaira Muhammad ne a ranar 8 ga watan Oktoban wannar shekarar.

Yadda matashi ya kona kakarsa da fetur

An ruwaito cewa Nura Mas'ud ya taho gidan da kakarsa ta ke ne dauke da man fetur a hannunsa.

Ana zargin cewa da zuwansa gidan ya kwararawa Zuwaira Muhammad man fetur daga nan kuma ya banka mata wuta.

Matashi ya amsa laifin kashe kakarsa

Yayin binciken yan sanda, Nura Mas'ud ya bayyana cewa lallai shi ya kona kakarsa, Zuwaira Muhammad.

Haka zalika ya kara da cewa ya yi haka ne saboda yadda kakarsa ta ke caccakarsa kan yadda yake saka tufafi da kuma rashin lafiya da yake fama da shi.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Bincike da aka fara ya nuna cewa Nura Mas'ud yana fama da tabin hankali kuma yana karɓar magani a asibitin Kazaure.

Yan sanda sun ceto yan jarida a jeji

A wani rahoton kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Anambra na nuni da cewa rundunar yan sanda ta yi nasarar ceto wasu yan jarida wajen yan bindiga.

An sace 'yan jaridar ne a hanyarsu ta zuwa filin wasan da Najeriya za ta kara da kasar Libiya daga Legas zuwa jihar Akwa Ibom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng