"An Bata Mani Suna:" Martanin Tsohon Sanata kan Zargin Fitar da Bidiyon Tsiraici

"An Bata Mani Suna:" Martanin Tsohon Sanata kan Zargin Fitar da Bidiyon Tsiraici

  • Tsohon Sanata, Elisha Abbo ya musanta zargin da ake na cewa ya yada bidiyon tsiraicin wata mata
  • Matar mai suna Wange David ta bayyana cewa tsohon Sanatan na da bidiyon ta da ya dauka tun a shekarar 2015
  • Kuma yanzu haka ya na mata barazana da bidiyon, har ma ya rika yada shi a kafar sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa - Tsohon sanatanda ya wakilci Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya yi martani kan ikirarin wata Wange David na cewa ya na sakin bidiyon tsofaffin yan matansa.

Sanata Elisha Abbo ya ce dukkanin abubuwan da aka rika yada cewa ya yi kalen sharri ne saboda kawai ya na a matsayin dan siyasa.

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi yadda ya kwaci Dauda Lawal daga hannun EFCC, ya kalubalance shi

Sen Ishaku Elisha Cliff
Tsohon Sanata ya harzuka kan zargin yada bidiyon tsiraici Hoto: Sen Ishaku Elisha Cliff
Asali: Facebook

A hirar da yi da Berekete Family TV ranar Talata,Sanatan ya ce an bata masa suna tare da jefa shi da abokansa cikin mawuyacin hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya musanta zargin yada bidiyon tsiraici

Tsohon Sanata Elisha Abbo ya ce babu kamshin gaskiya kan zargin da tsohuwar budurwarsa ta yi na cewa ya saki bidiyon tsiraicinta da ya dauka a shekarar 2015.

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Sanata Abbo ya ce Wange David ta yi masa sharri kan cewa ya na yi mata barazana da bidiyon da ya dauka.

Sanata Abbo ya nemi a ba shi hakuri

Lokacin da ya bayyana a cikin shirin, Sanatan ya zo da wasu shaidu da ke nuna cewa Ms. Wange ta bayar da labarinta a kansa a bai-bai.

Ya bayyana cewa tun bayan da ta fara yada labarin cewa ya na tura ta wajen abokansa domin ta mu'amalance su ya shiga halin damuwa.

Kara karanta wannan

"Na rantse da Kur'ani kan zargin ta'addancin Zamfara:" Matawalle ya yi martani

Zargin mu'amala da matar aure ya fusata Sanata

A baya kun ji cewa tsohon dan majalisa mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya, Sanata Elisha Abbo ya bayyana zargin da Wange David ke yadawa a matsayin sharri.

Tsohon dan majalisar ya nemi Wange David ta gaggauta janye kalamanta a cikin awanni 72 ko ya dauki hukuncin shari'a domin a bi masa hakkinsa da ta ke takewa a idon duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.