Ana Kuka da Tsadar Mai, Gwamna Ya Yi Magana kan Korar Ma'aikata

Ana Kuka da Tsadar Mai, Gwamna Ya Yi Magana kan Korar Ma'aikata

  • Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya musanta cewa gwamnatinsa na shirin korar wassu daga cikin ma'aikatan gwamnatin jihar
  • Gwamna Otti ya bayyan cewa ko kaɗan ba shi da shirin korar ma'aikata inda ya ƙara da cewa yanzu ya mayar da hankali ne wajen kyautata musu
  • Gwamnan ya kuma gargaɗi ma'aikatan da ke fashin zuwa wurin kan cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya yi magana kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa zai kori wasu ma'aikata a jihar.

Gwamna Alex Otti ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na korar wani ma’aikaci a jihar.

Gwamna Otti ya musanta shirin korar ma'aikata
Gwamna Alex Otti ya ce bai da shirin korar ma'aikata Hoto: @Alexotti
Asali: Facebook

Me Gwamna Otti ya ce kan korar ma'aikata?

Kara karanta wannan

Gwamna ya fallasa yadda shugaban al'umma ya karbi kudi aka hallaka mutane a yankinsa

Gwamna Otti ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a birnin Umuahia, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kyautatawa ma’aikatan gwamnatin jihar domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya kuma bayyana cewa biyan albashin ma’aikata a kan lokaci ya taimaka wajen ƙara zaburar da su kan aikinsu.

"Ban san daga ina jita-jitar ke fitowa ba. Babu wani batun korar ma'aikata. Ba mu ma yi tunanin hakan ba. Babu wani abu mai kama da hakan."
"Kamar yadda na faɗa ba mu da wannan shirin. Za mu ci gaba da tabbatar da cewa muna kyautatawa ma'aikata."

- Gwamna Alex Otti

Otti ya gargaɗi ma'aikata a Abia

Ya ɗora alhakin fargabar korar da ma'aikatan ke yi a kan halayyar wasu daga cikinsu na yin sakaci da aikinsu.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya ba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya yiwa ministocinsa

Gwamna Otti daga nan ya gargaɗi ma'aikatan gwamnati da suke ƙin zuwa wuraren aikinsu cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba.

Gwamna Otti ya rantsar da kwamishinoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya rantsar da kwamishinoni shida a wani yunkuri na yiwa majalisarsa garambawul.

Kwamishinonin sun karbi rantsuwar kama aiki daga babban lauyan gwamnati kuma sakataren dindindin na ma'aikatar sharia'a na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng