Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Kowane Musulmi Ya Sani Kan Ranar Ashura
- A gobe Talata ne ranar 10 ga watan Muharram 1446 wanda al'ummar Musulmi a fadin duniya ke gudanar da ibada a cikinta
- A addinin Musulunci, ana kiran ranar 10 ga watan Muharram da Ashura wanda ta samo tarihi tun zamanin Annabi Musa AS
- A wannan, rahoton Legit ta tatttaro muku muhimman bayanai kan abubuwan da suka shafi ranar Ashura da ibada a cikinta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A gobe Talata, 10 ga watan Muharram a kalandar Musulunci ne za a yi ranar Ashura a kusan duka fadin duniya.
Ranar Ashura ta kebanta da wasu abubuwa masu muhimmanci da suka shafi al'ummar Musulmi baki daya.
Legit ta tarrao muku wasu abubuwa masu muhimmanci da Sheikh Sale Al-Munajjid ya wallafa a shafinsa kan ranar Ashura.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin ranar Ashura a Musulunci
A ranar 10 ga watan Muharram ne Allah ya kubutar da Annabi Musa (Alaihissalam) da mutanensa daga sharrin Fir'auna.
Saboda haka suka riki ranar suna azumi domin nuna godiya kuma haka zalika Annabi Muhammad (SAW) ya umurci Musulmi su rika azumtar ranar.
Azumin Tasu'a da Ashura
Sai dai Annabi Muhammad (SAW) ya umurci al'ummarsa da su rika yin azumin kwanaki biyu; Tasu'a da Ashura.
Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana cewa yin azumin kwana biyun zai zamo hanyar da Musulmi za su saba da azumin Yahudawa da suke yi a ranar 10 ga wata kawai.
Muhimmancin azumin Ashura
Ya tabbata cikin hadisi cewa Annabi Muhammad (SAW) ya fadi cewa azumin Ashura na kankare zunubin shekara guda daya.
Haka zalika sai azumi ranar Tasu'a duk wanda ya yi shi zai samu ladan sabawa da al'adar Yahudawa.
Darasi cikin ranar Ashura
Yahudawa sun riki ranar Ashura suna azumi saboda nuna godiya ga Allah da ya ƙubutar da su daga sharrin Fir'auna.
Saboda haka ake bukatar al'ummar Musulmi su tuna da abin da ya faru na kubutar da Yahudawa kan cewa suma Allah zai iya kawo musu mafita a halin da suke ciki a yanzu.
Azumin Ashura lokacin tafiya
Duk da cewa Shari'a ta bayar da damar ajiye azumi a yayin tafiya wasu daga cikin magabata na yin azumi a ranar Ashura a halin tafiya.
Sun kuma fadi dalili kan cewa ita ranar Ashura babu damar sake azuminta idan ta wuce sabanin azumin Ramadan da ake iya ramawa.
Watanni hudu masu alfarma a Musulunci
A wani rahoton, kun ji cewa an shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 tun bayan hijirar Annabi mai tsira da aminci daga garin Makka.
Addinin Musulunci ya ware watanni hudu na musamman masu alfarma a cikin watanni 12 da kalandar Musulunci ta kunsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng