Ku sadu da kyawawan 'ya'ya matan Aliko Dangote (hotuna)

Ku sadu da kyawawan 'ya'ya matan Aliko Dangote (hotuna)

Tsawon shekaru da dama, mutane da dama suna la’ajabin su wanene ‘ya’ya matan mai kudin Afrika Aliko Dangote, abubuwan da sukeyi da sauransu. Idan kana tunanin wadannan yaran zasu kasance masu izza da nuna kai, toh kana bukatar sake tunani.

Ku sadu da kyawawan 'ya'ya matan Aliko Dangote (hotuna)
Aliko Dangote and 'ya'yansa mata

Duk da kasancewarsa babban attajiri kuma fittacen dan kasuwa, Aliko Dangote na da kyawawayn ‘ya’ya mata guda uku Halima Bello (babbar yar sa), Fatima da kuma Mariya Dangote, wadanda basu dauki duniya a bakin komai ba kuma basa duba arzikin mahaifinsu.

KU KARANTA KUMA: Bayan rade-radin mutuwa, gwamna Bello ya dawo Najeriya

Halima ta hada karatunta na digiri a fannin tallata kasuwanci daga jami’ar American Intercontinental University, Landan, da kuma Webster Business School, Landan. Sannan ta ci gaba a Webster Business School daga kammala karatunta na digiri domin hada digiri na biyu a fannin kasuwanci. Ta kuma auri wani mazaunin jihar Kano Sulaiman Sani Bello kuma suna da ‘ya’ya biyu tare. A yanzu haka tana aiki tare da mahaifinta a matsayin mai tsara dabarun kasuwanci (strategist).

Ku sadu da kyawawan 'ya'ya matan Aliko Dangote (hotuna)
Halima Dangote Bello tare da mahaifinta, Aliko Dangote.

A watan Afrilu na shekara 2015, Mariya Dangote ta samu digiri na biyu daga jami’ar Coventry University kuma tun lokacin ta samu kusanci mai karfi da mahaifinta. Duk da cewan ta fito daga gidan masu kudi, Mariya ta kasance mace mai kamala kuma bazaka taba ganinta a taron nuna kai ba ta gwamace ta ajiye kanta a sawwake.

KU KARANTA KUMA: Cikin kurkukun Kuje inda Fani-Kayode zai zauna

Ku sadu da kyawawan 'ya'ya matan Aliko Dangote (hotuna)
Aliko Dangote tare da iyalinsa a lokacin bikin kammala karatun Mariya a UK

A daya fannin kuma, Fatima Dangote wacce ta kasance daya daga cikin yaran attajirin dan kasuwan ta kasance tana gudanar da nata kasuwancin, inda take shugabantar wani kamfanin yin kananan kek (cupcake).

A halin yanzu yan matan uku suna da wani abu guda iri daya kuma wannan ne gaskiya, dukkansu sunyi karatu a jami’a mafi kyau a birnin Landan kuma bazaka taba ganinsu ba tare da sun rufe kansu da mayafi ba.

https://youtu.be/4e72lR1KgEQ

Asali: Legit.ng

Online view pixel