Kano: Bayan Nadin Dan Agundi, Tinubu Ya Nada Surukin Ganduje Babban Muƙami

Kano: Bayan Nadin Dan Agundi, Tinubu Ya Nada Surukin Ganduje Babban Muƙami

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin surukin shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje a matsayin hadiminsa
  • Tinubu ya naɗa Idris Ajimobi a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren kula da kiwon dabbobi a Najeriya
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 13 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na Facebook

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya naɗa Idris Ajimobi a matsayin hadimi na musamman.

Tinubu ya nada Ajimobi a matsayin hadiminsa a bangaren ci gaba da kula da kiwon dabbobi a Najeriya.

Tinubu ya ba surukin Ganduje babban muƙami na musamman
Bola Tinubu ya gwangwaje surukin Abdullahi Ganduje da mukami a matsayin hadiminsa. Hoto: @OfficialAPCNg.
Asali: Facebook

Tinubu ya ba surukin Ganduje mukami

Kara karanta wannan

Batun gyara ake: Tinubu ya sake kora a hukumomi, ya nada sabbin shugabanni a PenCom, NSITF

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris Ajimobi suruki ne ga tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje wanda ke auren ƴarsa mai suna Fatima.

Wannan nadin na zuwa ne bayan ƙirƙirar sabuwar ma'aikatar kula da dabbobi da shugaban ya yi a Najeriya.

Shugaban ya bukaci samun ci gaba a bangaren harkokin noma da inganta tattalin arziki a Najeriya.

Tinubu ya ce samun ci gaba a bangaren noma da bunƙasa tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi za su dakile rigima tsakanin makiyaya da manoma.

Tinubu ya sallami shugaban hukumar NPA

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan shugaban ya kori Mohammed Bello-Koko a matsayin shugaban hukumar NPA wanda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya naɗa.

Bayan sallamar Bello-Koko, Tinubu ya maye gurbinsa da Abubakar Dantsoho wanda zai zama shugaban hukumar nan take da ake sa ran zai shafe shekaru biyar kan kujerar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da nadin tsohon sanatan Kano da Dan Agundi manyan mukamai

Tinubu ya naɗa tsohon sanatan Kano mukami

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya naɗa Sanata Bashir Lado a matsayin hadiminsa na musamman.

Tinubu ya naɗa tsohon sanatan Kano ta Tsakiya a matsayin hadimi a bangaren da ya shafi Majalisar Dattawa.

Sanata Bashir Lado a baya ya taba rike mukamai babban daraktan hukumar yaki da safarar mutane ta NAPTIP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.