An Cafke Wasu Daga Cikin Masu Hannu a Tayar da Bam a Borno

An Cafke Wasu Daga Cikin Masu Hannu a Tayar da Bam a Borno

  • Wasu daga cikin ƴan ƙunar bakin waken da aka tura domin kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno sun shiga hannun hukumomi
  • An bayyana cewa sama da ƴan ƙunar baƙin wake mutum 30 aka tura zuwa Gwoza domin kai hare-haren ta'addanci
  • Hare-haren ƴan ƙunar baƙin waken dai ya yi sanadiyyar rasuwar aƙalla mutum 18 yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Hukumomi sun bayyana cewa an cafke wasu mata guda biyu ƴan ƙunar baƙin wake a jihar Borno.

An cafke ƴan ƙunar bakin waken ne dangane da tayar da bama-bamai a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar.

An cafke 'yan kunar bakin wake a Borno
'Yan kunar bakin wake mutum biyu sun shiga hannu a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Fashewar bama-baman dai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane aƙalla 18 tare da raunata wasu da dama.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun kwararo zuwa jihar Neja daga kasashen waje? An gano gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cafke ƴan ƙunar baƙin wake a Borno

Wani jami’in ƙaramar hukumar ya tabbatar da cafke ƴan ƙunar bakin waken ga tashar Channels tv.

Ya bayyana cewa daga cikin matan ƴan ƙunar baƙin waken guda 30, an tura su ne cikin Gwoza domin tayar da bama-baman a wurare daban-daban, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

A cewar wata majiya, ƴan ƙunar baƙin wake guda huɗu ne suka tayar da bama-bamai kawo yanzu.

Ta bayyana cewa ɗaya daga cikin ƴan ƙunar baƙin waken da ta fito daga yankin Pulka tana amsa tambayoyin da sojoji suke yi mata a shingen bincike, lokacin da ta firgita ta tayar da bam ɗin inda ta kashe kanta, soja da wani ɗan sa-kai.

An tattaro cewa matan sun shiga garin Gwoza ne daga wurare daban-daban, wasu daga Pulka wasu kuma daga tsaunin Mandara.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin bam a Borno, ya fadi matakin dauka

Dakarun sojojin sun kafa dokar hana fita a ƙaramar hukumar Gwoza sakamakon hare-haren.

Borno: Tinubu ya magantu kan harin bam

A wani labarin kuma, kun ji cewa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren bama-bamai da suka haddasa asarar rayuka da raunata wasu mutane da dama a ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

Shugaban ƙasar ya bayyana hare-haren a matsayin ayyukan ta'addanci, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta ƴan ta'addan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng