Karin Albashi: Shugaban Jam’iyyar Adawa Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Rika Biyan Ma’aikata

Karin Albashi: Shugaban Jam’iyyar Adawa Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Rika Biyan Ma’aikata

  • Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Shehu Gabam ya nemi a biya N100,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi
  • Shugaban jam’iyyar adawar yabayyana hakan ne a ranar Lahadi, inda kuma ya nemi gwamnati ta duba batun tallafin mai
  • Har yanzu an gaza cimma wata matsaya tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago a tattaunawa kan karin albashin ma'aikata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Shehu Gabam ya nemi a biya N100,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi tare da yin kira da a daidaita tallafin man fetur.

Jam'iyyar SDP ta yi magana kan mafi karancin albashi.
Shehu Gambam ya ba da shawarar sabon mafi karancin albashi. Hoto: Shehu Musa Gabam
Asali: Facebook
"A gare ni, abin da nake tunani a wannan gabar: Ya kamata gwamnati ta yi tayin kudin da ya haura N100,000."

Kara karanta wannan

Albashin ma'aikata: "Abin da ya kamata NLC da TUC su nema a wajen Tinubu" Jigon PDP

- In ji Shehu Gabam.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam’iyyar adawar yabayyana hakan ne a ranar Lahadi, a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin 'siyasar lahadi.'

Shehu Gabam ya ce:

“Abin da nake tunani ke nan. Tayi ne da kowa zai iya cewa an kamanta. Mutane za su samu damar shan iska, su je aiki ba tare da tunanin kassara ma'aikatu ba.
"Dole ne gwamnati ta sake duba wannan lamari na tallafin man fetur. Na sha ambatar hakan da dama, za a iya daidaita lamura idan aka daidaita tallafin mai da albashin."

Takaddama kan mafi karancin albashi

Har yanzu an gaza cimma wata matsaya tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago a tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi.

Wani mataki na yajin aiki da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka shiga a makon jiya ya tilastawa gwamnati komawa kan teburin tattaunawa.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

Shugabannin kwadago sun ki amincewa da tayin N62,000 na baya-bayan nan, daga N60,000, sun kuma dage a kan N250,000, inda suka rage kudin daga kudirinsu na N494,000 a baya.

Abin da ya kamata NLC ta nema - Akinni

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani jigon jam'iyyar PDP, Dare Akinniyi ya nemi 'yan kwadago da su sauya akalar bukatunsu ga gwamnati kan mafi karancin albashi.

Dare Akinniyi, ya dage kan cewa Najeriya ba za ta iya biyan biyan N250,000 a matsayin mafi karancin albashi ba amma ya ba 'yan kwadago shawarar abin da za su yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel