Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami'in Yan Sanda a Yayin Wata Musayar Wuta

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami'in Yan Sanda a Yayin Wata Musayar Wuta

  • Wasu miyagun ƴan binɗiga sun halaka mataimakin sufeton ƴan sanda (DSP) a yayin wata musayar wuta a jihar Delta
  • Dakarun sojoji sun samu nasarar cafke mutum shida daga cikin ƴan bindigan tare da raunata wasu mutum biyu
  • Sojojin sun kuma kwato kayayyaki a hannun ƴan bindigan waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin na halaka DSP na ƴan sanda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Wasu gungun ƴan bindiga a ranar Talata sun kashe mataimakin sufeton ƴan sanda (DSP), Sunday Okoebor, a birnin Asaba, babban birnin jihar Delta.

Sai dai, ƴan bindigan sun yi rashin sa’a yayin da sojojin Najeriya na Brigade 63 suka kama takwas daga cikinsu, inda biyu suka raunata sannan mutum biyu suka tsere, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa dakarun 'yan sanda wuta, sun halaka rayuka da yawa a jihar APC

Yan bindiga sun halaka DSP a Delta
Yan bindiga sun harbe DSP a jihar Delta Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Sojojin, sun sake yin tattaki zuwa maboyar ƴan ta’addan inda suka kama wasu mutum 125, takwas daga cikinsu mazauna yankin sun bayyana cewa waɗanda suke yi musu fashin kadarorinsu da kuma ta’addanci a yankunansu ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske kan wannan nasarar, Kanal lbrahim Gambari, babban hafsan hafsoshi na 63 Brigade a Asaba, ya ce mutanensa sun samu labarin kisan da aka yi a unguwar Koka, inda suka tattaru zuwa yankin.

A cewarsa, jami'ansa sun haɗu da ƴan sanda a atisayen ‘Operation Hawk’ inda suka yi musayar wuta da ƴan ta’addan yayin da wani ɗan kungiyar mai suna Aminu ya bindige DSP a wajen inda ya kashe shi nan take.

Sai dai, abin takaicin shi ne, biyu daga cikin masu laifin sun tsere da bindigu guda biyu, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan yan ta'adda a Taraba, sun ceto mutanen da suka sace

"Mun raunata mutum biyu, biyu sun tsere kuma mun sami damar kama wasu mutum shida. Mun kuma kama mutum 125 a maboyarsu inda takwas daga cikinsu aka gano ƴan fashi ne." A cewarsa.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da ƙaramar bindiga, kwamfutar tafi-da-gidanka, kayan ado, wayoyi, da sauran kayayyaki.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Ƴan Sanda

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan ƴan sanda da ke a wani shingen bincike a jihar Imo.

A yayin harin ƴan bindigan sun halaka biyu daga cikin jami'an ƴan sandan ne mahaɗar titunan Ahiara a ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise, jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel