Jerin abubuwa 20 da basa karya azumi
A yayin da al'ummar musulmai na duniya suka fara gabatar da azumi ranar Lahadi 5 ga watan Mayu, 2019, majiyarmu LEGIT.NG ta gabatar da wani bincike akan wasu abubuwa da suke ciwa al'ummar musulmai tuwo a kwarya, musamman ma a nan gida Najeriya
Mutane da yawa suna samun sabani akan wasu abubuwa da suke ganin kamar suna karya azumi idan sunyi, sai dai kuma a binciken da majiyarmu ta gabatar ta gano cewa akwai abubuwa kimanin 20 wadanda da mutane ke tunanin suna karya azumi, amma ba sa karyawa.
Ga jerin abubuwan mun kawo muku a kasa:
1. Shakar turare ko yin amfani da shi a jikin kaya: Addini ya yadda mai azumi ya shaki turare a kowanne lokaci mutukar ba a sha ba.
2. Fitar jini daga baki ko hanci: Shari'a ta aminta mutum ya cigaba da azumin shi, idan jini ya fito daga bakin shi ko hanci, mutukar ba a hadiye shi ba.
3. Ga masu cutar Asthma, suna iya amfani da abin shakarsu idan bukatar hakan ta taso.
4. Cirewar hakori: Shi ma an yarda mutum ya cigaba da azumin shi, idan har jinin da ya fita sanadiyyar fitar hakorin bai kai ciki ba.
5. Gwajin jini: Sai dai idan har jinin ya kasance daidai da adadin jinin da aka cire a jikin mutum.
6. Abin shakar hanci: Ga masu mura suna iya amfani da shi, matukar dandanon maganin bai kai ga zuwa makogwaron mutum ba.
7. Fitar jini daga hanci: Shi ma ba ya karya azumi, har sai idan hakan ta faru da gangan da ganganci.
8. Dandana abinci: Shari'a ta yadda masu dafa abinci su dandana mutukar ba za su bari dandanon abincin ya shiga cikin su ba.
9. Karya, rantsuwa ko zagi: Duk da dai wadannan abubuwan suna rage ladan azumi, amma shari'a ba ta ce suna karya azumi ba.
10. Yin mafarkin da ruwan maniyyi ya fita: Shari'a ta bukaci mutum ya ta shi ya yi wankan janaba ya cigaba da azumin shi.
KU KARANTA: Tsawon lokutan da mutane ke yi da azumi a bakin su a kasashen duniya
11. Yin amfani da man wanke baki: Shari'a ta ba da damar wanke baki da man wanke baki, amma kuma ta yi gargadi da yin amfani da man wanke baki mai karfi wanda dandanon sa zai iya kai wa makoshin mutum.
12. Amai: Amai ba ya karya azumi, sai dai idan har an yi shi da gangan.
13. Sumba, da runguma: An yadda ma'aurata su sumbaci junan su sannan kuma su rungumi junan su mutukar hakan ba za ta kai su ga yin jima'i ba.
14. Aski, ko yankan farce: Su ma ba sa karya azumi.
15. Wanka: Idan mutum ya hadiyi ruwa a lokacin wanka ba da gangan ba, zai cigaba da azumin shi, kamar yadda shari'a ta tsara.
16. Lalle: Yin lalle ga mata ba ya karya azumi.
17. Wanka a kogi: Mutum zai iya yin wanka a kogi, hakan ya hallata, amma kuma shari'a ta yi gargadi akan hakan, saboda ya na da matukar hadari.
18. Allura: An yadda a yiwa mutum allura, mutukar ba ta abinci ba ce.
19. Kwalliya: An aminta ayi kwalliya lokacin da ake azumi.
20. Maganin ciwon ido na digawa: An yadda mai azumi ya yi amfani da maganin ciwon ido na digawa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng