An Yi Garkuwa da Babban Malamin Addini a Kaduna, Rundunar ’Yan Sanda Ta Magantu

An Yi Garkuwa da Babban Malamin Addini a Kaduna, Rundunar ’Yan Sanda Ta Magantu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta yi magana yayin da aka samu rahoton 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani malamin addini
  • An ruwaito cewa an sace shugaban cocin St. Thomas Parish ne a rukunin gidajen malaman majami'ar da sanyin safiyar Lahadi
  • Yayin da majamami'ar ta hada kai da jami’an tsaro domin a kubutar da malamin, an nemi mabiya su kwantar da hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da Rabaran Gabriel Ukeh, shugaban cocin St. Thomas Parish da ke unguwar Zaman Dabo a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

'Yan sanda sun yi magana kan rahoton garkuwa da malamin addini
'Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addini a Kaduna. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

An ruwaito cewa an sace limamin cocin ne a rukunin gidajen malaman majami'ar da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Basaraken Arewa ya sha da ƙyar a hannun 'yan bindiga, 'yan sanda sun kai masa ɗauki

An yi garkuwa da malamin addini

Babban malami, Rabaran Emmanuel Kazah, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai wadda jaridar Punch Online ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabaran Emmanuel Kazah, ya ce:

“Yayin da muke neman addu’o’i domin malamin ya kubuta, muna kuma yin Allah wadai da wannan aika-aikar na garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
"Haka zalika muna kira ga gwamnati da ta karfafi guiwar jami’anta na leken asiri a yanzu da muke tunkarar bukukuwan Sallah domin bankado shirin 'yan ta'adda da dakile su."

'Yan sandan Kaduna sun magantu

A yayin da shugabannin majamami'ar suka hada kai da jami’an tsaro domin a kubutar da malamin, Rabaran Kazah ya yi kira ga mabiyansu da su guji daukar doka a hannunsu.

Rabaran Kazah ya jaddada cewa ba za su yi kasa a guiwa ba wajen ganin Rabaran Gabriel Ukeh ya dawo gare su cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sandan Kano ta yi namijin aiki, an damke miyagu iri iri

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ce, zai tabbatar da labarin tare da fitar da bayani.

'Yan bindiga sun farmaki basarake

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai hari gidan Sarkin Ninzo, Alhaji Umar Musawa da ke karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya shaidawa manema labarai cewa sun kai dauki ga basaraken amma har yanzu ba a san inda uwar gidansa take ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel