Albashin Ma’aikata: “Abin da Ya Kamata NLC da TUC Su Nema a Wajen Tinubu” Jigon PDP

Albashin Ma’aikata: “Abin da Ya Kamata NLC da TUC Su Nema a Wajen Tinubu” Jigon PDP

  • An nemi shugabannin NLC da TUC da su kasance masu yin hangen nesa game da bukatarsu ta neman sabon mafi karancin albashi
  • Wani jigon PDP, Dare Akinniyi, ya dage kan cewa Najeriya ba za ta iya biyan biyan N250,000 a matsayin mafi karancin albashi ba
  • Da yake magana da Legit.ng a ranar Lahadi, jigo a PDP ya lissafa wasu bukatu 4 da ya kamata ma'aikata su gabatar wa gwamnatin Tinubu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kakakin kungiyar matasan jam’iyyar PDP ta kasa, Dare Glintstone Akinni, ya bayyana bukatu hudu da ya kamata kungiyoyin kwadago su gabatar wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Jigon PDP ya yi magana kan mafi karancin albashi
Jigon PDP ya ba 'yan kwadago shawara kan mafi karancin albashin ma'aikata. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Twitter

Akinniyi ya ce bukatar ma’aikata ta N494,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ba abu ne mai yiwuwa ba idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Kara karanta wannan

A ina gwamnan Edo ya ga N70,000 na mafi karancin albashi? Shehu ya taso gwamnoni a gaba

Tirka-tirkar karin mafi karancin albashi

A baya kun ji cewa kungiyar kwadago ta NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwan ta TUC sun gabatar da N494,000 a matsayin mafi karancin albashi ga gwamnatin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai shugaba Tinubu ya ki amincewa da wannan bukatar inda ya yi tayin biyan albashin da ya haura N60,000. Daga nan 'yan kwadago suka sauko zuwa N250,000.

A halin yanzu dai gwamnatin tarayya ta yi tayin biyan N62,000 amma gwamnonin Najeriya sun ki amincewa da hakan kan cewa ba za su iya biyan ma’aikata N60,000 ba.

"Abin da ya kamata ma'aikata su yi" - Akinni

A wata hira da jaridar Legit.ng ta wayar tarho a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni, Akinniyi ya bukaci ma’aikata su kasance masu hangen nesa a bukatunsu.

Kara karanta wannan

NLC: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya kawo mafita kan mafi ƙarancin albashi a jihohi

Akinniyi ya bayyana buƙatu huɗu da ya kamata ma’aikata su mikawa gwamnati maimakon ƙarin albashi:

"1. 'Yan kwadago su nemi gwamnati ta dawo da farashin man fetur zuwa 60 ko 80 a kan kowace lita
"2. 'Yan kwadago su nemi gwamnatin tarayya ta sanya tallafi a harkar karatu.
"3. 'Yan kwdago su nemi gwamnati ta yi karin mafi karancin albashi zuwa N60,000-N100,000.
4. A janye karin kudin wutar da aka yi, sannan a dawo da biyan tallafin kudin wutar kamar yadda ya ke a baya."

Albashin N62,000: Shehu Sani ya magantu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan sabon tayin gwamnatin tarayya na N62,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Shehu Sani ya ce N62,000 na nufin N10,000 ga kowacce shiyyar siyasa daga shiyyoyi shida na kasar, yayin da N2000 ke wakiltar babbar birnin tarayya (FCT).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel