Matsin Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fadi Abin da Talakawa za suyi wa Shugabanni

Matsin Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fadi Abin da Talakawa za suyi wa Shugabanni

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya shawarci 'yan Najeriya su rubanya addu'o'i ga shugabanninsu domin samun sauki
  • Sarkin ya hori shugabanni su zage damtse wajen jagoranci na gari kamar yadda su ka yi alkawari saboda 'yan kasar nan sun matsu su ga sauyi
  • Yce kara da cewa raba Najeriya ba zai taba zama mafita ga matsalar tsaro ba, tare da shawartar shugabanni su gaggauta magance matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Nassarawa-Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya shawarci 'yan Najeriya su taya shugabanninsu da addu'a domin samun waraka da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Jama'a sun ƙosa a yanzu": Sarkin Musulmi ya kuma jan hankalin shugabanni

Sa'ad Abubakar ya bayyana haka ne a taron bikin cika shekaru biyar na Sarkin Lafiya, Mai Shari'a Sidi Bage-Mohammed, mai ritaya a karagar mulki.

Sarkin Musulmi, mai Alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya shawarci shugabanni su sauke nauyin al'ummarsu Hoto: The Sultan Of Sokoto Palace
Asali: Facebook

Mai alfarman ya ce yan Najeriya sun kosa su samu sauyi mai kyau a yanayin yadda rayuwarsu ke tafiya ta yau da kullum, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya shawarci shugabanni kan mulki

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya hori shugabanni kan su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu wajen ci gaban al'umma.

Ya ce duk da ana sane da irin kokarin da gwamnati ke yi, amma 'yan Najeriya sun kosa su ga sauyi mai kyau, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Sarkin Musulmin ya ce sanannen abu ne cewa kasar nan na fama da matsalar tsaro, inda ya kara da cewa raba kasar nan ba zai taba magance matsalar da ake fuskanta ba.

Kara karanta wannan

Ya kamata Najeriya ta jagoranci kasashen Afrika a girman tattalin arziki, Shehu Sani

Shugaban ya jaddada muhimmancin masu mulki su gaggauta nemo mafita kan matsalolin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.

"An kaucewa tsarin Allah," Sarkin Musulmi

Mun ruwaito muku a baya yadda Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce kaucewa tsarin da Allah Ya wajabtawa musulmi na daga manyan dalilan shiga matsala a Najeriya.

Ya ce za a samu mafita amma sai an tuba, an koma ga Allah (SWT), sannan a dage da yin addu'ar neman sauki, inda ya yi bayanin cewa Allah ba zai shiga lamarin wanda ba ya bauta masa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel