Bayanai Sun Fito Game da Shirin Tinubu da Sabon Tsarin Albashin Ma’aikata

Bayanai Sun Fito Game da Shirin Tinubu da Sabon Tsarin Albashin Ma’aikata

  • Take-take na nuna kwamitin sabon tsarin albashi zai kammala duk zaman da zai yi kafin a shiga watan Mayun 2024
  • Abin da ake tunani shi ne kwanan nan Bola Tinubu zai sanar da mafi karancin albashin da za a koma amfani da shi
  • Idan kwamitin ya kammala aikinsa, shugaban Najeriya zai yi amfani da ranar ma’aikata wajen yi wa jama’a albishir

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Alamu na nuna watakila Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon tsarin albashi a ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa.

Kungiyoyin kwadago suna tattaunawa da gwamnati domin ganin an fito da tsarin albashi a dalilin tsadar rayuwar da aka shiga a kasar.

Kara karanta wannan

Zargin cushe a kasafi: Tinubu ya dira kan Sanata Ningi, ya kwance masa zani a kasuwa

Bola Tinubu
Watakila Bola Tinubu ya sanar da sabon karin albashin ma’aikata a Najeriya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Bola Tinubu da karin albashin ma'aikata

Rahoton da Punch ta kadaita da shi zuwa yanzu ya nuna watakila shugaban kasar yana shirin sanar da matsayar da za a dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu zai zabi 1 ga watan Mayu ne domin ita ce ranar kwadago ta duniya.

Yaushe sabon tsarin albashi zai fara aiki?

Jaridar ta ce babu mamaki za a dawo da dokar baya ta yadda za ta fara aiki tun daga Afrilu, sai a biya ma’aikata bashin albashin.

Bisa al’ada, shugaban kasa ya kan yi jawabi a ranar ma’aikata a Najeriya. Ana tunani Tinubu zai yi maganar karin a wannan rana.

Kwamitin karin albashi yana ta aiki

Kwamitin karin albashin yana bakin kokari wajen ganin an kammala tattaunawa ta yadda za a iya sanar da karin zuwa lokacin.

Wani daga cikin ‘yan kwamitin sabon tsarin albashin ya shaidawa jaridar cewa za su sake yin zama a mako mai zuwa da mai bi masa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

Kamar yadda ya bayyana ba tare da ya bari an kama sunansa ba, ya ce bayan nan kwamitinsu zai fara jin ra’ayoyin sauran jama’a.

Da zarar an kammala sauran ta bakin al’umma, kwamitin zai san inda ya dosa domin ganin an gama komai kafin farkon Mayu.

Ana biyan N35, 000 a kan albashi

Ana da labari zuwa yanzu gwamnati tana biyan ma’aikata karin N35, 000, kila kafin karewar wa’adin a Maris, an kawo sabon tsari.

Da zarar an iya cin ma matsaya, ana kyautata zaton sabon tsarin albashi zai fara aiki, sai a biya ma'aikata cikon na watannin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel