Muhimman Abubuwa 10 da Musulmi Ya Kamata Ya fi Ba Kulawa a Watan Ramadan

Muhimman Abubuwa 10 da Musulmi Ya Kamata Ya fi Ba Kulawa a Watan Ramadan

A yau Juma’a 22 ga watan Maris, al’ummar Musulmi suka dauki azumi na 12 domin bin umarnin Allah madaukakin sarki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yayin da aka shiga watan Ramadan, Malaman Musulunci su na yawan gargadin Musulmai da su kauce wa abubuwa da dama yayin azumi.

Abubuwan da Musulmi ya kamata ya fi ba su kulawa a watan Ramadan
Ana bukatar Musulmi ya yawaita karatun Alkur'ani a watan Ramadan. Hoto: MICHELE SPATARI/AFP, Emmanuel Osodi/Majority World/Universal Images Group.
Asali: Getty Images

Har ila yau, akwai wasu abubuwa da mutum zai ba su kulawa na musamman a wannan wata da muke ciki domin samun tsira, a cewar Premium Times.

A wannan rahoto, Legit Hausa ta kawo muku muhimman abubuwa 10 da ya kamata Musulmi yafi ba su kulawa a watan Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Daukar nauyin ta'addanci: Sheikh Gumi ya fadi abin da ya dace a yi wa Tukur Mamu

1. Yawan karanta Alkur’ani

Malamai suna yawan kiran Musulmai da su ba da lokacinsu sosai wurin karanta Alkur’ani mai girma.

Mafi yawan makaranta Al’kur’ani ko ba a lokacin azumi ba suna daga cikin mafi daraja a cikin al’umma bare lokacin azumi da ake rubanya lada.

2. Yawan ambaton Allah

Ana bukatar Musulmi ya yawaita ambatin Allah a kowane lokaci domin samun tsira, cewar rahoton MuslimSG.

Yawan ambaton Allah ya kunshi zikiri da addu’o’i da karatun Alkur’ani da kuma salatin Annabi Muhammad (SAW).

3. Ciyarwa da sadaka

Daga cikin manyan ayyuka da ake samun lada akwai yawan sadaka a lokacin azumin watan Ramadan.

Har ila yau, ana bukatar Musulmai su kasance cikin masu ciyarwa musamman ga wadanda ba su da karfi.

4. Ziyara ga marasa lafiya

Yawan ziyara a kowane lokaci malamai sun tabbatar da cewa ya na kara tsawon rai ga dan Adam.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

Ana bukatar Musulmi su yawaita kai ziyara musamman ga marasa lafiya a asibiti ko a gidajensu, cewar Arabian Tongue.

5. Sallar dare a Ramadan

Sallar dare wanda aka fi sani ‘Lailatul Kadri’ musamman a goman karshen azumi ya na kusanto da dan Adam ga Ubangiji.

Ana so Musulmi ya yawaita sallar dare domin neman kusanci ga Ubangiji da kuma samun biyan bukatu.

6. Sallah a kan lokaci

Sallah ita ce babbar ibadah da aka ba muhimmanci ga Musulmi ba sai a lokacin watan azumi ba.

Dole mai yin azumi ya ba sallah muhimmanci musamman kula da lokuta da kuma zuwa jam’i.

7. Gudunmawa ga Musulunci

Akwai ayyukan raya Musulunci da ake bukatar kowane Musulmi ya ba da karfi domin samun lada.

Ayyukan raya addinin Musulunci suna da yawa kama daga aikin agaji da karatuttuka da kuma daukar nauyin karatuttuka a rediyo da talabijin.

8. Gyara mua’amala

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi malamin Musulunci 1 da suke goyon bayan ya tattauna da ƴan bindiga

Ana yawan samun matsala ta gaba a tsakanin al’ummar Musulmai ko kuma akidu daban-daban, cewar Amaliah.

Malamai suna yawan gargadin mutane da su tabbatar sun nemi yafiyar juna musamman a watan azumi.

9. Zakkar fidda-kai

Wannan ita ce zakka da ake ba marasa karfi a ranar Idin salla domin samun yadda za su yi da rayuwarsu.

Ana bukatar mutum ya fitar da abin da ya fi ci a gidansa domin taimakon talakawa marasa karfi.

10. Soyayyar juna

Kamar yadda aka fada a baya, ya kamata Musulmai su yafewa juna musamman a wannan wata.

Musulunci addini ne na zaman lafiya wanda ya kamata Musulmai su yada soyayya da kawar da gaba a tsakaninsu.

Abubuwa 10 da mai azumi zai kaucewa

Kun ji cewa ya kamata mai azumi a kowane lokaci ya kauracewa wasu abubuwa musamman a wannan wata na azumi.

Wannan rahoto ya jero muku abubuwa 10 da Musulmi ya kamata ya kauracewa a watan azumi mai albarka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel