Daukar Nauyin Ta'addanci: Sheikh Gumi Ya Fadi Ya Fadi Abin da Ya Dace a Yi Wa Tukur Mamu

Daukar Nauyin Ta'addanci: Sheikh Gumi Ya Fadi Ya Fadi Abin da Ya Dace a Yi Wa Tukur Mamu

  • Sheikh Ahmad Abubakar Mahnud Gumi ya yi magana kan zargin ɗaukar nauyin ta'addanci da ake yi wa Tukur Mamu
  • Malamin addinin musuluncin ya buƙaci da a yi masa hukuncin da ya dace idan har an same shi da laifin da ake tuhumarsa da shi
  • Ya yi nuni da cewa tun da lamarin yana gaban kotu, kuskure ne a sanya shi cikin jerin masu ɗaukar nauyin ta'addanci, domin hakan hurumin kotu ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya ce ya kamata a hukunta Mallam Tukur Mamu, idan aka same shi da laifin ta’addanci.

Mamu na hannun jami’an tsaro na farin kaya (DSS) tun bayan da aka kama shi a birnin Alƙahira, babban birnin ƙasar Masar, a watan Satumban 2022.

Kara karanta wannan

Daukar nauyin ta'addanci: Sheikh Gumi ya fadi yadda miyagun ke samun kuɗi

Sheikh Gumi ya yi magana kan batun Tukur Mamu
Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci a hukunta Mamu idan yana da laifi Hoto: @IU_Wakili
Asali: Twitter

A ranar Laraba ne labari ya bayyana cewa an sanya sunan Mamu tare da wasu mutum 14 a cikin jerin masu ɗaukar nauyin ta’addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da yake magana a wani shiri a shafin X da jaridar Daily Trust ta shirya a ranar Laraba, Shehin malamin ya ce hukumomin tsaro ba su da hurumin bayyana wani a matsayin mai ɗaukar nauyin ta’addanci.

Ya ce tun da shari’ar na gaban kotu, alhakin hakan ya rataya ne a wuyan kotu ba hukumomin tsaro ba, rahoton jaridar Nigerian Tribune ya tabbatar.

Me Sheikh Gumi ya ce kan Mamu?

Gumi ya ce abin da ya faru tsakanin Mamu da jami’an tsaro lamari ne ƙarara na rashin fahimtar juna, amma bai so ya ce komai a kai ba a halin yanzu tunda shari’ar tana gaban kotu.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

A kalamansa:

"Al’amarin Mamu yana gaban kotu. Mu jira mu ji daga kotu. Ba daidai ba ne a riƙa yi masa shari'a a kafafen yaɗa labarai. Mu jira kotu ta bayyana cewa shi mai ɗaukar nauyin ta'addanci ne ko a'a.
"Ina tunanin idan aka wanke shi, yana da ƙwakkwarar hujjar da zai shigar da ƙara kan ɓata masa suna.
"Ku kawo hujjojinku, kuma idan aka samu Mamu da laifi, ya kamata a yi masa hukuncin da ya dace. Amma game da abin da na sani, mu jira kotu kawai."

Gumi ya buƙaci gwamnati ta sauya salo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana kuskuren da gwamnati ke yi wajen yin amfani da ƙarfi wajen yaƙar ƴan bindiga.

Malamin addinin musuluncin ya buƙaci a sauya salo ta hanyar amfani da sulhu domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel