Ka san nawa ne farashin Dala a Yau?

Ka san nawa ne farashin Dala a Yau?

Bayan dogon lokaci dai darajar Naira na ta kara sama tun daga sama da N500 har zuwa N360 Legit.ng na samun labari cewa yanzu kuma farashin dalar ya dan kara tashi

Ka san nawa ne farashin Dala a Yau?
Farashin Dala ya tashi a Yau

Farashin dala ya kara tashi bayan an dauki dogon lokaci dalar na yin kasa. An dai dauki kusan wata guda darajar dalar in ban da kasa kurum ba abin da yake yi. Da sai da darajar Dalar ya haura N500.

Sai dai daga jiya zuwa yau Naira ce ta sha kasa a kasuwar Duniya inda ta yi kasa a kan Dala daga kan N382 zuwa N385. Dalar Pounds ta Ingila kuwa dai ta kai N400 yanzu a kasuwar ‘yan canji kamar yadda Legit.ng ke samun labari.

KU KARANTA: An damke wani Attajiri saboda satar kudin mai

Ka san nawa ne farashin Dala a Yau?
Gwamnan CBN Emefiele

Cikin wata guda kawo yanzu dai dala tayi wani mugun kifewa daga sama da N500 zuwa N360 a bankuna kwanakin bay kamar yadda muka rahoto. A wannan makon ne bankin kasar watau CBN ya bada umarni bankuna su rika sayarda dala a kan N360.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar nan dai na murmurewa bayan ya ruguje a baya. Da alamu dai abubuwa sun dan fara mikewa a Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekaru 2 da zaben shugaba Buhari; Ya abubuwan su ke a yanzu?

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng