An Zargi Sanatan PDP da Yunkurin Juyin Mulki a Majalisa, an Samu Karin Bayani

An Zargi Sanatan PDP da Yunkurin Juyin Mulki a Majalisa, an Samu Karin Bayani

  • Sanata Opeyemi Bamidele daga mazabar Ekiti ta tsakiya ya zargi Sanata Abdul Ningi da yunkurin juyin mulki a majalisar dattawa
  • Bamidele ya yi ikirarin cewa Ningi ya zargi majalisar da yin cushe a kasafin 2024 kawai don tunzura 'yan majalisar da bata mata suna
  • Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta dakatar da SanataNingi, daga Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku kan kalamansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Sanata Micheal Opeyemi Bamidele daga mazabar Ekiti ta tsakiya ya zargi Sanata Abdul Ningi da yunkurin "juyin mulkin farar hula", bayan ya yi ikirarin cewa an yi cushe a kasafin 2024.

Opeyemi Bamidele ya yi zargin cewa Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya yi yunkurin yi wa shugaban majalisar Godswill Akpabio juyin mulki.

Sanata Ningi na yunkurin yin juyin mulki - Sanata Opeyemi Bamidele
Sanata Opeyemi Bamidele ya zargi Sanata Ningi da yunkurin juyin mulki. Hoto: @Sen_AbdulNingi
Asali: Twitter

Shugaban masu rinjaye a majalisar ya yi ikirarin cewa Ningi yana kokarin tunzura kungiyar Sanatocin Arewa su yi wa Akpabio juyin mulki, wanda ya karbi mulki daga hannun Ahmad Lawan.

Kara karanta wannan

Dakatar da Sanata Ningi: Tinubu ya sanya labule da shugabannin majalisa, bayanai sun fito

Kalaman Sanata Bamidele a kan Ningi

A cikin wani faifan bidiyo da majalisar dattawa ta wallafa a shafin Facebook, an jiyo Bamidele yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan abin da babban yayana, Sanata Abdul Ningi ya shirya ko ya yi niyyar yi, tamkar juyin mulkin farar hula ne wanda kuma bai samu nasara ba.
"Ubangiji ya yi albarka ga duk wadanda suka ware kansu daga kungiyar sanatocin Arewa, domin Ningi ya so ya yi amfani da su domin cin ma kudurinsa."

Kalli bidiyon a kasa:

Me yake faruwa a majalisar dattawa?

A karshen makon da ya gabata, Sanata Abdul Ningi ya yi hira da wani gidan talabijin, inda ya yi zargin cewa an yi cushen biliyoyin Naira a kasafin kudin 2024.

Sai dai 'yan majalisar dattawa ba su dauki wannan zargi na Ningi da wasa ba, inda aka kusa ba hammata iska a zauren majalisar a yau Talata, 12 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Ningi: Majalisa ta dauki mataki kan Sanatan da yayi zargin cushen N3tr a Kasafin 2024

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an tayar da hazo sosai a majalisar, inda ake zargin kungiyar Sanatocin Arewa da Ningi ke jagoranta na shirya wata makarkashiya ne a kan lamarin.

An dakatar da Sanata Abdul Ningi

Legit Hausa ta kuma rahoto cewa a zaman majalisar na yau, aka dakatar da Sanata Abdul Ningi, daga Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku.

Kudurin majalisar ya biyo bayan zargin da Ningi ya yi na cewar an yi cushe Naira tiriliyan 3 a cikin Naira Tiriliyan 28.7 na kasafin kudin 2024.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da dakatar da Mista Ningi bayan da mafi rinjayen sanatoci suka goyi bayan kudirin dakatarwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel