An Shiga Jimami Bayan Shugaban Jam'iyyar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Bayan Shugaban Jam'iyyar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta yi babban rashi a jihar Ekiti bayan shugabanta na jihar ya yi bankwana da duniya
  • Sai dai ba a bayyana musabbabin mutuwar Mista Paul Omotoso ba wanda ya yi bankwana da duniya a safiyar ranar Laraba, 6 ga watan Maris
  • Sai dai, rahotanni sun ce tun bayan da aka yi garkuwa da marigayin a shekarar 2023, yake ta fama da rashin lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ado-Ekiti, jihar Ekiti - Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ekiti, Paul Omotoso ya rasu.

Omotoso ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 6 ga watan Maris, 2024, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Shugaban jam'iyyar APC ya rasu
Jam'iyyar APC ta rasa shugabanta a jihar Ondo Hoto: @ekititrend
Asali: Twitter

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a san musabbabin mutuwarsa ba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da dalibi ya rasa ransa a Abuja, an fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta tattaro cewa marigayi shugaban jam'iyyar baya cikin ƙoshin lafiya tun bayan lokacin da aka yi garkuwa da shi a watan Yulin shekarar 2023.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC a jihar, Segun Dipe ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai iya bayar da ƙarin bayani kan musabbabin mutuwar marigayin da kuma inda aka ajiye gawarsa ba.

Ya halarci tarurrukan APC a ranar Litinin

Jaridar Daily Post ta kawo rahoto cewa marigayin ya halarci tarurrukan siyasa daban-daban a ranar Litinin, 4 ga watan Maris 2024.

Daga nan ne ya yi ƙorafin rashin lafiya a ranar Talata, inda aka garzaya da shi zuwa asibitin gwamnati da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar inda a nan ne kwanansa suka ƙare.

Wani 'dan APC ya rasu a Bayelsa

Jigon jam'iyyar APC a jihar Bayelsa, Mista Terry Tukuwei, ya rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya ritsa da shi.

Kara karanta wannan

Rayuka da dama sun salwanta yayin da aka samu barkewar rikici, bidiyo ya fito

Marigayin wanda shi ne daraktan yaɗa labarai na kwamitin kamfen ɗin APC a jihar, ya rasu ne lokacin da yake kan hanya daga garin Nembe zuwa ƙauyen Okoroba don halartar kamfen ɗin jam'iyyar.

Jigon Jam'iyyar APC Ya Rasu a Delta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban jigo a jam'iyyar APC a jihar Delta, Cairo Ojougboh, ya yi bankwana da duniya.

Marigayin wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne ya rasu ne yayin da yake tsaka da kallon wasan Najeriya da Afirika ta Kudu a gasar cin kofin AFCON 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel