FAAC: Yadda Aka Rabawa Gwamnoni da Ministan Abuja Naira Tiriliyan 6.5 a Shekara 1
- An raba sama da Naira tiriliyan 6 daga asusun tarayya na FAAC daga Junairu zuwa Disamban 2023
- Daga kason FAAC ne gwamnoni da kananan hukumomi su ke samun kudi bayan harajin da aka karba
- Jihohi masu arzikin danyen mai sun fi tashi da kaso mai tsoka domin ana yi masu karin 13% dabam
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A kowane wata, kwamitin FAAC da ke aikin rabon kudi ya kan zauna domin yin kason abin da gwamnatin Najeriya ta samu.
Ana raba wannan kudi tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi da kananan hukumomi.
An yi rabon N6.57tr a FAAC
A wani rahoto da aka samu daga The Cable, an yi bayanin abin da kowace jiha ta tashi da shi daga kason N6.57tr da aka raba a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ake ba 52.68%, sai a rabawa gwamnatocin jihohi 26.72%, a karshe kananan hukumomi 774 su na samun 20.60%.
Kudin jihohi masu arzikin mai
Jihohin da ke da arzikin danyen mai su kan samu karin 13% idan an raba kudi a FAAC. Duka jihohin nan suna kudancin kasar ne.
Jaridar ta ce Delta ta samu N483bn a shekarar bara, yayin da Ribas ta zama ta biyu da N426.8bn, sai Akwa Ibom ta karbi N380.10bn.
Kano mai kananan hukumomi 44 ta samu kudi mai yawa duk da ba ta da arzikin fetur. Gombe, Ebonyi da Ekiti kuwa su ne a baya.
Wasu jihohi da yawa ba za su rayu idan aka janye rabon da ake yi daga asusun FAAC ba. Birnin tarayya Abuja ta samu kusan N150bn.
Ga yadda aka yi rabon FAAC a 2023:
1 Delta N483.57bn
2 Ribas N426.84bn
3 Akwa Ibom N380.1bn
4 Legas N371.39bn
5 Bayelsa N268.34bn
6 Kano N261.37bn
7 Oyo N207.37bn
8 Katsina N191.43bn
9 Borno N176.94bn
10 Kaduna N170.91bn
11 Jigawa N170.74bn
12 Benuwai N161.99bn
13 Edo N161.69bn
14 Anambra N161.54bn
15 Ondo N156.33bn
16 Neja N155.62bn
17 Imo N152.39bn
18 FCT N145.3bn
19 Sokoto N146.19bn
20 Bauchi N144.98bn
21 Kebbi N143.93bn
22 Osun N141.48bn
23 Adamawa N139.14bn
24 Kogi N136.97bn
25 Enugu N133.29bn
26 Abia N125.92bn
27 Yobe N124.14bn
28 Taraba N123.05bn
29 Filato N121.71bn
30 Ogun N120.72bn
31 Zamfara N119.17bn
32 Kuros Riba N118.8bn
33 Kwara N115.11bn
34 Nasarawa N111.54bn
35 Ekiti N107.5bn
36 Ebonyi N107.45bn
37 Gombe N99.05bn
Ina maganar hako mai a Arewa?
An rahoto Shehu Umar Buba ya ce an yi watsi da kokarin hako danyen mai a yankin Arewacin Najeriya daga rijiyoyin Kolmani.
Sanatan ya zauna da shugaban NNPC, Mele Kyari da NSA, Malam Nuhu Ribadu a kan maganar, za a cigaa da aikin cikin watan nan.
Asali: Legit.ng