An Shekara 1 Shiru, Sanata Ya Fadi Halin da Ake Ciki Wajen Hako Danyen Mai a Arewa

An Shekara 1 Shiru, Sanata Ya Fadi Halin da Ake Ciki Wajen Hako Danyen Mai a Arewa

  • Shehu Umar Buba ya yi bayanin inda aka kwana a kokarin ganin jihohin Arewa sun samu arzikin mai
  • Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hako mai a Kolmani da ke tsakanin Bauchi da Gombe
  • Sanatan Kudancin Bauchi ya ce an gamu da tsaiko a aikin, amma za a cigaba a cikin watan nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Bauchi - Shehu Umar Buba mai wakiltar kudancin Bauchi a majalisar dattawa, ya yi karin haske game da aikin hako mai a Kolmani.

Daily Trust ta ce Shehu Umar Buba ya ce kamfanin NNPCL sun yi alkawarin cigaba da yunkurin samar da mai daga rijiyoyin Kolmani.

Kolmani
Rijiyar man Kolmani Hoto: @MBuhari, @Dolusegun16
Asali: Twitter

Ina labarin rijiyoyin man Kolmani?

Sanata Shehu Umar Buba ya yi wannan bayani ne da yake amsa tambayoyi a wajen manema labarai ranar Litinin a garin Bauchi.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan majalisar ya ce masu ruwa da tsaki a Bauchi da Gombe sun damu da lamarin rijiyoyin man da aka gano a shekarun nan.

Shehu Umar Buba wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattawa ya ce yana zuwa majalisa ya fara bijiro da batun man.

Kolmani: Kokarin Sanata Shehu Baba

Sanata Shehu Buba yake cewa sun nemi jin dalilin da ya sa aikin ya tsaya tun bayan da Muhammadu Buhari ya kaddamar a 2022.

An rahoto Sanatan yana bayanin yadda suka yi zama da jami’an gwamnatin tarayya da ‘yan majalisu domin farfado muhimmin aikin.

Yadda Sanata Baba suk yi da gwamnati

"A lokacin da aka rantsar da mu a majalisar dattawa, rijiyoyin man Kolmani ne babban abin da na so in kawo kudiri a kai,"
"Amma sai na tuntubi wasu masu ruwa da tsaki musamman NNPC ta wajen Mele Kyari, NSA, Malam Nuhu Ribadu da ‘yan majalisun jihohin da abin ya shafa, sai mu ka yi zama da Kyari game da hako rijiyoyin man Kolmani."

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan rasuwar shahararren jarumin fina-finai a Najeriya da shekaru 81

"Mun bukaci sanin meyasa tun da tsohon shugaan kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da rijiyoyin man, aka yi watsi da ayyuka a wurin."
"Shugaban NNPC ya ba mu bayanai masu gamsarwa. Yanzu NNPC ya bada kwangila ga wani kamfanin Indiya da sun shigo kasar, ana ta shirye-shirye."

- Shehu Usman Baba

A watan nan za a fara aiki, idan Fabrairu ta wuce shiru, Sanatan ya ce za su fito fili su yi magana kuma za su yi amfani da zauren majalisar tarayya.

Kolmani zai sa a samu danyen mai a Arewa

A karshen 2022 aka ji labari Muhammad Buhari ya hallara kauyen Kolmani domin a fara aikin hako danyen mai a karon farko a Arewa.

Kwatsam sai aka ji wani Abdullahi Tamatuwa yana yi wa jihar Bauchi barazanar cewa zai je kotu, ya ce rijiyoyin a Gombe suka fada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel