Watanni da Sauka, Masani Ya Tona Yadda Buhari Ya Jefa Tinubu a Ramin Tashin Dala

Watanni da Sauka, Masani Ya Tona Yadda Buhari Ya Jefa Tinubu a Ramin Tashin Dala

  • A lokacin Muhammadu Buhari yana mulki, ana zargin an karbi bashin N23tr a hannun bankin CBN
  • Da aka zanta da Nnaemeka Obiareri, ya zargi gwamnatin tarayya da batar da wannan kudi a iska
  • A watanni takwas rak da Bola Tinubu ya yi a karaga, an karbo bashin kusan N8tr a cewar Obiareri

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - An zargi Muhammadu Buhari da yin asarar bashin N23tr da gwamnatin tarayya ta karba daga hannun babban bankin CBN.

A hirar da aka yi da shi a tashar Arise, Nnaemeka Obiareri ya zargi gwamnatin baya da batar da N23tr, a karshe sai aka sayo Daloli da su.

Buhari
Bola Tinubu da Muhammadu Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Bola Tinubu zai binciki Buhari?

Masanin ya ce ya kamata a ji yadda aka yi da kudin da CBN ya buga ya ba Buhari, yana ganin akwai bukatar Bola Tinubu ya bincika.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nnaemeka Obiareri wanda masani ne a bangaren tattalin arziki ya zargi gwamnati mai-ci ta Bola Ahmed Tinubu da buga wasu N7.8tr.

Duk da wadannan kudi da aka buga, masanin tattalin ya ce har yanzu ana cin bashi alhali an nuna za ayi ban-kwana da aron kudi.

Da gangan aka tashi kimar Dala

Obiareri yana ganin cewa matsin lambar da Dalar Amurka ta ke fuskanta ba na hakika a ne, wasu ne su ka sace kudin al'umma.

Tribune ta rahoto kwararren yana bada shawarar a canza fasalin tattalin arzikin kasar, ya ce ba za a cigaba ba idan ba ayi hakan ba.

Tun daga 1991 lokacin da Janar Ibrahim Badamasi yake mulki, Obiareri yana ganin tukin gangan aka rika yi wa Najeriya har zuwa yau.

Masanin wanda yana da kware kan harkar banki ya ce matsalar kasar tana bukatar sai an fara daga yi wa tsarin mulki garambawul.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

Ya Tinubu zai gyara Najeriya?

"Ko da an kawo waliyyi a kasar nan, ba zai iya shawo kan ta a irin tsarin mulkin da muke tafiya a kai ba.
60% na matsin lambar da ake samu ta bangaren Dala a kasuwa yau na rashin gaskiya ne."

- Nnaemeka Obiareri

#BuyNaijaToGrowTheNaira

Ana da labarin Ben Murray Bruce ya kawo shawarar a koma amfani da kamfanin Glo domin kiran waya da hawa yanar gizo a Najeriya.

Sanata Ben Murray Bruce ya ce dole a koma cin kayan Dangote kuma a rika tuka Innoson idan da gaske ake so kimar Dalar ta karye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel