FAAC: Jihohi 5 da suka samu kason kudi mafi tsoka a shekarar 2020
Nigeria kasa ce da ta dogara kan kudaden da ake samu daga siyar da man fetur duk da cewa Allah ya albarkaci kasar da wasu ma'adinai da za su iya samar mata da kudaden shiga.
Duk wata, kwamitin rarraba kudade na gwamnatin tarayya, FAAC, na raba wa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi kudaden da aka tattara a asusun kasar daga haraji da wasu abubuwan.
Bisa alkalluman da aka wallafa daga Hukumar Kiddiga ta Kasa, NBS, Business Day ta ruwaito cewa a shekarar 2020, FAAC ta bawa gwamnatin tarayya jimillar n2.49 tiriliyan yayin da jihohi sun samu N2.30 tiriliyan a cikin shekarar.
DUBA WANNAN: Pantami da NSA sun sha banban kan batun ƙaddamar da fasahar 5G a Nigeria
Ga jerin jihohin biyar da suka fi samun kaso mafi tsoka a duk wata daga gwamnatin tarayyar kama yadda rahoton ya wallafa.
1. Jihar Delta - N186.828 biliyan
2. Jihar Akwa Ibom - N141.187 biliyan
3. Jihar Rivers - N141.187 biliyan
4. Jihar Bayelsa - N116.401 biliyan
4. Jihar Legas - N115.932 biliyan
A wani rahoton, alkalluman NBS ya nuna cewa tsawon shekaru biyu, jihohi 11 cikin 36 a kasar ba su samu masu saka hannun jari daga kasashen waje ba.
KU KARANTA: Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa
Legit.ng ya gano cewa jihohin ba su iya samun masu saka hannun jari daga kasahen waje ba a 2019 da 2020 a cewar rahoton na NBS.
Jihohin sune Bayelsa, Ebonyi, Ekiti, Gombe, Jigawa, Kebbi, Kogi, Plateau, Taraba, Yobe da Zamfara.
A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.
Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng