Ya Zabi 1: An Bukaci Tinubu Ya Sallami Ministansa Kan Dalili 1 Tak, Bayanai Sun Fito

Ya Zabi 1: An Bukaci Tinubu Ya Sallami Ministansa Kan Dalili 1 Tak, Bayanai Sun Fito

  • Babban Daraktan hukumar CODE, Hamzat Lawal ya bukaci Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan Minista Nyesom Wike
  • Hamzat ya ce ya kamata Wike ya dauki nauyin duk abin da ke faruwa ganin shi ne gwamnan Abuja ba na Rivers ba
  • Hamzat ya bayyana haka ne yayin hira da Legit inda ya ce Wike na hada siyasa da kuma hada mulkin birnin Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – An bukaci Shugaba Tinubu ya sallami Ministan Abuja, Nyesom Wike kan matsalar tsaro.

Babban Daraktan hukumar CODE, Hamzat Lawal ya bukaci Shugaba Tinubu ya dauki mataki idan har ba a samu sauyi ba.

Kara karanta wannan

Garba Shehu ya fadi kuskuren da 'yan Najeriya suka yi wa Buhari, ya roki kada a maimaita wa Tinubu

An kirayi Tinubu ya sallami Ministansa kan abu daya
An Bukaci Tinubu Ya Sallami Minista Wike Kan Dalilin Tsaro. Hoto: Bola Tinubu, Hamzat Lawal, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Mene Hamzat ke cewa kan Wike?

Lawal ya ce ya kamata Wike ya dauki nauyin duk abin da ke faruwa ganin shi ne gwamnan Abuja ba na Rivers ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hamzat ya bayyana haka ne yayin hira da Legit inda ya ce Wike na hada siyasa da kuma hada mulkin birnin Abuja.

Ya ce:

“Wike ya na dauka har yanzu shi ne gwamnan jihar Rivers, ya kamata ya yanke hukuncin ci gaba da siyasar Rivers ko kula da Abuja.
“Ya kamata ya sani shi ne mai mulkin Abuja idan aka samu matsala mulkin Tinubu ne ta samu matsala, don haka ba zai yiwu ba."

Matsalar rashin tsaro a Abuja

Ya kara da cewa:

“Wike damuwarsa siyasar Rivers ce wanda ke dauke hankalinsa kan abin da ya kamata ya yi a Abuja.”

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da babban birnin tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

Idan ba a manta ba, a ‘yan kwanakin nan an yi ta samun muggan hare-haren ‘yan bindiga a birnin Abuja, cewar Premium Times.

A ‘yan kwanakin nan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wasu ‘yan gida daya da suka hada da mata shida da wani namiji.

Pantami ya yi magana kan tsaro

Kun ji cewa, tsohon Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya yi martani kan matsalar rashin tsaro yayin da ta kara kamari.

Pantami ya ce a matsayinsa na tsohon Minista yafi kowa jin kunci ganin yadda matsalar ke karuwa.

Wannan na zuwa ne yayin da matsalar ta yi yawa a babban birnin Tarayya Abuja a ‘yan kwanakn nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel