Pantami Ya Bayyana Babban Abin Da Ke Damunsa Kan Rashin Tsaro, Ya Ce an Tafka Shirgegen Kuskure

Pantami Ya Bayyana Babban Abin Da Ke Damunsa Kan Rashin Tsaro, Ya Ce an Tafka Shirgegen Kuskure

  • Farfesa Isa Pantami ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka yi watsi da tsarin dakile matsalar tsaro a kasar
  • Pantami ya ce a lokacin da ya ke Minista ya kawo tsarin hada lambobin NIN da layukan mutane don irin wannan matsalar
  • Tsohon Ministan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin 15 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka yi watsi da tsarin da ya kawo.

Pantami ya ce a lokacin da ya ke Minista ya kawo tsarin hada lambobin NIN da layukan mutane don irin wannan matsalar, cewar vanguard.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanya labule da shugabannin tsaron Najeriya kan dalili 1 tak, bayanai sun fito

Pantami ya bayyana babban kuskuren da aka yi kan harkar tsaro
Pantami ya ce fuskanci barazana kan tabbatar da tsarin. Hoto: Isa Ali Pantami.
Asali: Twitter

Mene Pantami ke cewa kan tsaro?

Ya ce amma abin takaici jami'an tsaro ba sa amfani da wannan tsarin don tabbatar da inganta tsaro a kasar baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin 15 ga watan Janairu.

Har ila yau ya ce ya gwada amfani da tsarin don tabbatar da dakile tsaro tare da kamo 'yan ta'adda kuma ya yi nasara.

Ya kara da cewa amma a abin takaici masu ruwa da tsaki sun ki amfani da tsarin don tabbatar da hana 'yan ta'addan sakat a kasar.

Wace shawara Pantami ya bayar?

Ya ce:

"Tsarin hada lambar NIN da layukan wayoyi ya na aiki, ya kamata wadanda ke da alhakin yakar rashin tsaro a tuntube su don yin amfani da tsarin.
"Rashin amfani da tsarin shi ne babbar matsalar ba wai tsarin ba, lokacin da na ke ofis na san lokuta har sau uku da aka yi amfani da su kuma an yi nasara.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar kula da da’ar ma’aikata

"A bangaren rashin amfani da tsarin, ina jin bakin ciki fiye da kowa saboda rayuwata ta shiga barazana saboda kaddamar da tsarin."

Pantami ya ce ya fuskanci barazana a fili da gidajen jaridu har ma BBC Hausa inda ya ce ya fi kowa jin bakin ciki duk da sadaukar da ransa da ya yi kan tsarin.

A karshe ya yi addu'ar ubangiji ya tserartar da wadanda suke hannun 'yan bindiga ya kuma kawo karshen matsalar baki daya.

Pantami ya samu abokinsa da zai biya kudin fansa

A wani labarin, Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya ce ya nemo wani abokinsa da zai biya kudaden fansa.

Wasu 'yan bindiga sun bukaci miliyoyin kudade bayan sace 'yan gida daya mata guda shida a birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel