Shehu Sani Ya Yi Shagube Ga Betta Kan Alkawarinta Na Fitar da Yan Najeriya Miliyan 50 Daga Talauci

Shehu Sani Ya Yi Shagube Ga Betta Kan Alkawarinta Na Fitar da Yan Najeriya Miliyan 50 Daga Talauci

  • Sanata Shehu Sani ya yi shagube ga Betta Edu sakamakon dakatar da ita da aka yi kan badakalar kudi naira miliyan 585
  • Tsohon dan majalisar ya tunatar da yan Najeriya cewa ajandar sabonta fata na gwamnatin Tinubu bai cimma nasara ba a ma’aikatar Betta Edu
  • Sai dai kuma, yan Najeriya sun garzaya dandalin soshiyal midiya don bayyana ra'ayoyinsu kan furucin Sani

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya sake caccakar Betta Edu, ministar jin kai da kawar da talauci, kwanaki bayan dakatar da ita.

Ku tuna cewa a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi umurnin dakatar da ministar nan take, kan zargin tafka badakalar kudi naira miliyan 585 a ma'aikatarta.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi martani kan dakatar da Betta Edu, ya aika gagarumin sako ga Tinubu

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta Edu
Shehu Sani Ya Yi Shagube Ga Betta Kan Alkawarinta Na Fitar da Yan Najeriya Miliyan 50 Daga Talauci Hoto: Dr. Betta Edu Media Watch, Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

A cewar wata sanarwa daga kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale, badakalar sun hada da zargin amincewa da biyan daruruwan miliyoyin naira zuwa wasu asusun ma'aikatan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani ya yi martani ga ci gaban ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu.

Ya bayyana cewa an cire ministar da ta yi alkawarin fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci karkashin gwamnatin Tinubu, daga kungiyar.

Sani ya rubuta:

"An cire matar da ke son fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci a watanni 40 daga kungiyar."

Yan Najeriya sun yi martani yayin da Sani ya yi shagube ga Betta Edu

Kamar kullun, yan Najeriya sun yi martani ga furucin tsohon sanatan a sashin sharhi na dandalin X.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Minista ya magantu bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa, bayanai sun fito

@legend_082 ya rubuta:

"Na san dan damfara da zaran na ga daya."

@olakayode15 ya rubuta:

"Ya kamata a shafe ma'aikatar an kafa ne don azurta yan tsirarun mutane maimakon talakawan yan Najeriya."

@EbukaNw82866148 ya rubuta:

"Ta fitar kimanin miliyan400 daga kungiyar sannan ta ruguza jirgin kungiyar kamar Titanic."

@Martolexx ya rubuta:

"Ya kamata mata su bar wa maza siyasa magana ta kare."

Obi ya magantu kan badakalar Betta Edu

A gefe guda, dan takararjam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi, ya yaba ma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, kan dakatar da ministar jin kai, Betta Edu kan badakalar naira miliyan 585.

A wasu jerin rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa dakatar da Betta Edu bai wadatar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel